Header Ads

An kammala zaɓe a Turkiyya, yayin da ake tsaka da zargin yin shisshigin ƙasashen waje a cikin sa

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da matarsa, Emine Erdogan, a yayin da suke jefa kuri'a a rumfar zaben su da ke Istanbul da ke kasar Turkiyya da safiyar ranar Lahadi

An kammala kada kuri'u a zaben kasar Turkiyya kuma ana gaf da fara kirga kuri'a, wannan zabe dai wani babban zabe ne a Turkiyya wanda zai kara wa'adin mulkin shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, wanda shine shugaban kasa mafi dadewa kan mulki a kasar, ko kuma ya kawo karshen ikon sa daga madafun iko.

An dai fara zaben 'yan majalisu da na shugaban kasar ne da karfe 8:00 na safe (0500GMT) an kuma kammala da karfe 5:00 na yamma (0400GMT) inda kusan mutane miliyan 64 ne suka cika ka'idojin yin zabe, a cikinsu mutane miliyan 3.4 ne za su yi zabe daga kasashen waje kusan kuma mutane miliyan 6 a wannan karon ne za su fara yin zaben.

Zaben wani babban kalubale ne ga Erdogan, wanda ke fuskantar dan takarar gamayyar adawa, Kemal Kilicdaroglu, a yayin da ake tsaka da fuskantar matsin tattalin arzuki da kuma abinda girgizar kasar ranar 6 ga watan Mayu ta haifar. 

Sakamakon zaben zai iya tsanza alkiblar siyasar kasashen waje da ta cikin gidan Turkiyya, wadanda abubuwa ne da ba a iya hasashen su a kasar mai mutane miliyan 85 kuma mamba a kungiyar hadakar tsaro ta NATO.

Tuni dai shugaban kasar na Turkiyya ya kada kuri'arsa a rumfar zaben sa Uskuda da ke Istanbul.

"Fata na shine bayan an kammala kirga kuri'u a wannan yammacin, sakamakon zaben ya kasance mai kyau ga Turkiyya da kuma makomar damakaradiyyar mu." Kamar yadda ya shaidawa manema labaru.

"Abu mai muhimmanci shine mutanen yankunan da girgizar kasa ta shafa suna kada kuri'unsu, kuma hakan na faruwa a yanzu. Zuwa zabe na da amfani domin nuna karfin damakaradiyyar Turkiyya. In Allah Ya yarda, za ta kasance rana mai cike da natsuwa ga damakaradiyyar Turkiyya." Kamar yadda ya bayyana bayan jefa kuri'arsa.

Shima babban abokin takarar shugaban kasar, Kilicdaroglu, ya jefa kuri'arsa a rumfarsa da ke babban birnin kasar ta Turkiyya, Ankara.

"Na yi alkawarin ruwan korama zai gudana." Kilicdaroglu , mai shekaru 74, ya bayyana bayan jefa kuri'arsa.

"Dukkaninmu mun rasa damakaradiyya. Mun rasa kasancewa a tare. Za ku ga korama ta zo wannan kasar bayan yau kuma za ta cigaba da zuwa." Kamar yadda Kilicdaroglu ya bayyana.

A zaben, in har ba dan takarar da ya samu sama da kashi 50 na kuri'u, to za a sake maimaici a ranar 28 ga watan Mayu.

Kilicdaroglu ya yi ikirarin cewa yana da tabbatattun hujjoji da ke nuna cewa kasar Rasha ta yi shisshigi a cikin zaben na Turkiyya ba tare da nuna kowacce hujja domin tabbatar da ikirarin nasa ba.

A bangaren kasar ta Rasha, kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov, a ranar Asabar ya bayyana cewa, "Mun yi watsi da zarge-zargen yin shisshigi a cikin zaben kasar Turkiyya. Wannan wani abu ne da ba zai faru ba kuma bai cancanci a tattauna shi ba." Inda ya bayyana cewa Kilicdaroglu ba zai iya kawo hujjojin ikirarin yin shisshigin ba domin "ba su a hakikanin zahiri."

A daya bangaren a yayin da ya ke jawabi a wani yanki mai suna Umraniye da ke Istanbul, shugaban kasar ta Turkiyya ya yi magana kan wani jawabi da shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya yi a cikin watan Janairun shekarar 2020, inda ya ce ya kamata Washington ta taimakawa wadanda ke adawa da Erdogan su yi nasara a kansa ta hanyar zabe, inda ya bayyana cewa ba za a cire shi ta hanyar juyin mulki ba.

"Biden ya bayar da umarni a cire Erdogan, na san haka. Duka mutane na sun san haka." Shugaban na Turkiyya ya bayyana, inda ya kara da cewa, "In kuwa haka ne, to kuri'un gobe za su bayar da amsa ga Biden."  

Erdogan din ya yi suka ga jawaban Kilicdaroglu a kan Rasha, inda ya bayyana Moscow a matsayin babbar kawa ga Ankara, "Rasha na daya daga cikin kawayenmu masu matukar amfani dangane da kayayyakin aikin noma." Kamar yadda ya nuna.

No comments

Powered by Blogger.