Header Ads

An kai hari ofishin jakadancin Katar a Sudan yayin da hare-haren jiragen sama suka girgiza Khartoum

Hayaki ya tashi saman wasu gine-gine bayan hare-haren jiragen sama a yakin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro na RSF a Khartoum North, Sudan

Hare-haren jiragen sama da musayar harbe-harben manyan bindigogi sun girgiza babban birnin kasar Sudan, Khartoum, a ranar Asabar, 20 ga watan Mayu, a yayin da kuma wasu mutane dauke da bindigogi suka yi kaca-kaca da ofishin jakadancin kasar Katar a yaki da ake cigaba da yi tsakanin janarorin kasar Sudan da ke kokarin neman iko.

Mutanen da ke zaune a Khartoum sun shaidawa kafar watsa labaru ta AFP cewa fada mai karfin gaske ya barke duk da kiraye-kirayen da kasashen waje ke yi na a tsagaita wuta domin kawo kayan agaji. Yankin da ke kusa da ginin gidan talabijin din kasar da ke birnin Omdurman wanda ke kusa da Khartoum na cikin wuraren da hare-haren suka shafa.

A ranar ta Asabar, ofishin jakadancin kasar Katar ya zama ofishin diflomasiyya na baya-bayan nan wanda aka kaiwa hari, hakan kuwa ya jawo yin Allah wadai daga Doha. "Kasar Katar ta yi Allah wadai da kakkausar murya da kutsawar da sojojin da ba kan ka'ida suke ba suka yi cikin ginin ofishin jakadancin ta da ke Khartoum tare da lalata kayan da ke ciki." Kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen kasar ta Katar ta bayyana.

"An kwashe ma'aikatan ofishin jakadancin tun tuni... Ba daya daga cikin jami'an diflomasiyya ko ma'aikatan ofishin jakadancin da suka samu wata cutarwa." Ma'aikatar ta bayyana tare da sake yin kira da "a kawo karshen fadan na Sudan cikin gaggawa, kasancewa cikin takatsantsan ... Da tseratar da rayukan fararen hula daga fuskantar wahalhalu sakamakon fadan." 

Kasar Katar ba ta bayyana dakarun Daglo na RSF kai tsaye da cewa sune ke da alhakin harin ba, sai dai a cikin wani jawabi daga hukumomi magoya bayan Burhan sun dora alhakin kai tsaye kan dakarun na RSF.

Yaki a kasar ta Sudan ya barke ne a tsakanin shugaban sojoji, Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa wanda ya zama abokin adawa, Mohamed Hamdan Daglo, wanda shine shugaban dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF) a ranar 15 ga watan Afirilun shekarar 2023. 

Rikicin ya haifar da rasa rayukan daruruwan mutane, mafiyawancinsu fararen hula tare da raba wasu sama da miliyan 1 da muhallansu. Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa wahalhalun yanayin rayuwa na kara hauhawa a kasar wadda ita ce ta uku a girma a nahiyar Afirka, wadda dama tuni daya cikin mutane uku na kasar sun dogara ne da kayan agaji tun kafin yakin.

No comments

Powered by Blogger.