Header Ads

Amurka na kashe biliyoyi kan yaƙi tare da kyale wahalhalun ruwan sha a Amurka - wasu mazauna jihar Mississippi

Ruwa mai duhu na fitowa daga bakin wani fanfo da ke cikin wani gida a Mississippi wanda ke nuni da wahalhalun ruwa a jihar.

Ran mutane na kara baci a jihar Amurka ta Mississippi saboda rashin ruwan sha sakamakon kayan aiki marasa kyau, inda wasu mazauna jihar suka bayyana cewa gwamnatin Amurka na kashe biliyoyin daloli a kan yaki da makamai tare da kyale 'yan kasarta.

Dubunnan daruruwan mazaunan an bar su ne da ruwa mai tabo da ke fitowa daga fanfunansu, inda suka rasa wani zabi illa su yi amfani da ruwan roba.

Kamar yadda kungiyoyin hakkin bil-adama suka bayyana, 'yan Afirka Amerikawa za su fi shan wahalar, domin suna rayuwa ne a wuraren da mafi yawa talakawa ne ke rayuwa kuma wuraren na da matsalar kayayyakin masu kyau da suka shafi ruwa da kuma rashin samar da isassun kadude.

Saboda kasa samar da kayayyaki bayan tsufan da wadanda ke nan suka yi, mazaunan birnin wadanda mafi yawansu bakar fata ne sun kwashi shekaru suna fama da daukewar ruwan tare da yi masu gargadin su tafasa ruwa akai-akai, hade da abubuwan da suka shafi lalacewar ruwa kamar "Lead" da kuma "E.coli bacteria."

Kamar yadda rahotanni suka nuna, wahalhalun ruwan na faruwa ne sakamakon raguwar saka jari a cikin kayayyakin da suka shafi ruwa a cikin shekarun da suka gabata.

A shekarar 2021, majalisar Congress ta amince da dalar Amurka tiriliyan 1.2 domin yin ayyuka, tare da tura kusan dalar Amurka biliyan 4.46 zuwa Mississippi a cikin shekaru biyar masu zuwa inda fadar White House ta fitar da ina kuma yaya kudin za su je Mississippi din na wucin gadi.

To sai dai aikin ya cigaba a hankali inda jihar ba wai kawai ta kasa samar da taimakon kudi a bangaren ayyuka ba ne amma ta ma bayar da hutun karbar haraji na kudaden shiga da mutane ke samu na dalar Amurka miliyan 542, wannan kuwa ya rage kudade ga kasafin kudin ta, ciki har da na gudanar da ayyuka.

A yayin da Amurkawa ke fama da rashin kudade a cikin watan da ya gabata, shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya sanar da taimakon soji ga kasar Ukraine har na dalar Amurka miliyan 375 duk kuwa da gargadi da kasar Rasha ta yi.

Amurka da kawayenta kasashen yamma na cigaba da samar da makamai masu yawa ga Ukraine tun bayan fara yakin na Ukraine a shekarar da ta gabata, wanda kamar yadda Rasha ta bayyana shi ya sa yakin bai zo karshe ba.

Kasar ta Rasha dai ta sha yin gargadi ga kasar Amurka kan samar da makamai ga Ukraine da kuma ruruta wutar yaki.

No comments

Powered by Blogger.