Header Ads

Almajiran Sheikh Zakzaky da ke Minna sun yi muzaharar Allah wadai da El-Rufai kan rushe-rushen da ya yi a Kaduna

Wasu muzahara a Minna


Almajiran shugaban harkar musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, da ke Minna a jihar Neja sun yi muzaharar Allah wadai da rushe-rushen da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufai, ya ke yiwa makarantun Fudiyya na Harka Islamiyya da gine-ginen 'yan uwa almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky a jihar Kaduna. 

An yi muzaharar ne da safiyar ranar Litinin 22 ga watan Mayu na shekarar 2023 wadda ta yi daidai da 2 ga watan Zhul-Qha'adah shekara ta 1444 bayan hijira.

 Mutane da dama ne dai suka halarci muzaharar da aka yi, inda wasu daga cikin su suke dauke da hotunan shugaban harkar musuluncin a Nijeriya da kuma tutocin Falasdinu.

No comments

Powered by Blogger.