Header Ads

Allah ya yi wa wakilin jaridar Almizan Malam Sabo Ahmad rasuwa

Marigayi Mal. Sabo Ahmad 
Allah ya yi wa daya daga cikin wakilan jaridar Almizan, Malam Sabo Ahmad, rasuwa a yau Alhamis, 18 ga watan Mayu na shekarar 2023.

Malam Sabo Ahmad ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya da ya yi kuma ya kasance wakilin jaridar Almizan da ke zaune a garin Samarun Zaria.

Kafin rasuwar marigayin, ya daukaka har ya zama Edita a jaridun Leadership Hausa.

Marigayin na da mata biyu da 'ya'ya maza da mata. 

Za a yi jana'izar sa a ranar Juma'a, 19 ga watan Mayu na shekarar 2023 da karfe 10:00 na safe a Mangwarori, Samaru. 

Allah ya jikansa da gafara.

No comments

Powered by Blogger.