Header Ads

Akwai yiwuwar mutane sama da 800,000 su bar kasar Sudan saboda fadan da ake yi a cikin ta - Majalisar ɗinkin duniya

Wasu mutane da suka gujewa rikicin kasar Sudan bayan sun iso filin jirgin sama da ke Dubai a cikin jirgin kwashe mutane a ranar 29 ga watan Afirilun shekarar 2023.

Akwai yiwuwar mutane sama da 800,000 su bar kasar Sudan sakamakon fadan da ake yi a tsakanin bangarorin sojoji biyu, a ciki har da wadanda suka zo nan a matsayin 'yan gudun hijira, kamar yadda wani jami'in majalisar dinkin duniya ya bayyana a ranar Litinin.

"Idan ba a samar da matsaya ba cikin gaggawa ga wannan rikicin, za mu ga mutane da yawa wadanda za su bar kasar domin su tsira da kuma neman taimako." Raouf Mazou ya bayyanawa a yayin wani taro a Geneva.

"A tattaunawar da muka yi da duka gwamnatocin da abin ya shafa da kuma wadanda muke aiki a tare da su, yawan da muka kayyade shine mutane 815,000 wadanda ka iya ficewa kasar ta Sudan zuwa kasashe bakwai makwafta." 

Kididdigar ta hada da mutane 580,000 'yan kasar Sudan da kuma wasu daga kasar Sudan ta Kudu da kuma wasu wuraren.

A yanzu haka, mutane 73,000 sun fice zuwa makwaftan kasar Sudan bakwai: Sudan ta Kudu, Chadi, Misra, Eritrea, Habasha, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Libiya.

A yayin taron, mai kula da ayyukan jin kai a kasar Sudan na majalisar dinkin duniya, Abdou Dieng, ya bayyana cewa halin da mutane ke ciki "na neman ya ta'azzara" kuma hatsarin fadawa cikin wasu kasashen abun damuwa ne.

"Yanzu sama da sati biyu kenan ana yin wannan mummunan yaki, yakin da ke sa halin da mutane ke ciki na kara ta'azzara." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.