Header Ads

A karon farko Majalisar dinkin duniya ta yi taron tuna ranar da aka kori Falasdinawa kusan 75,000 daga muhallansu domin kirkirar Isra'ila

Wasu Palasdinawa da aka tilastawa hijira

A karon farko a tarihinta, majalisar dinkin duniya za ta yi taron da a wannan karon na 75 kenan na tunawa da "Nakba Day" ko "Day of Catastrophe (Ranar Bala'i)", wato ranar da aka kirkiri kasar Isra'ila sakamakon raba Falasdinawa kusan 75,000 da muhallansu.

Kamar yadda kafar watsa labarun Falasdinawa ta WAFA ta bayyana, kwamitin majalisar dinkin duniya da ke tabbatar da hakkokin Falasdinawa (CEIRPP) zai shirya wata babbar tattaunawa a ranar Litinin daga karfe 10:00 na safe zuwa 12:20 na rana (agogon New York).

Taron, wanda za a yi a cibiyar majalisar dinkin duniya da ke New York, shine irinsa na farka da majalisar ta duniya ta yi.

Wadanda za su kasance a taron sune shugaban kwamitin, Ambasada Cheikh Niang, na kasar Senegal kuma zai hada da jawabi daga shugaban kasar Falasdinawa, Mahmoud Abbas. 

Manyan jami'an majalisar dinkin duniya da kuma wakilan kungiyoyin bangarori da na kungiyoyin fararen hula su ma za su yi jawabai domin ranar ta Nakba.

Bayan haka, za kuma a yi wani taro na musamman kan al'amarin a zauren majalisar daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 8:00 na dare.

Taron na so ya yi karin haske ne a kan yadda sojojin Isra'ila suka tsara share biyu cikin uku na mutanen Falasdinawa daga shekarun 1947 zuwa 1949, ta hanyar nuna wakoki a bayyane, hotuna, bidiyoyi da kuma jawabai daga mutane.

"Wannan taro ne domin nuna cewa manufofin adalci da zaman lafiya na bukatar sanin hakika da tarihin wahalhalun mutanen Falasdinawa da kuma tabbatar da hakkokin su da ba za a iya cirewa daga garesu ba." Kwamitin na CEIRPP ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.