Header Ads

Yemen ta haramta shigo da kayayyaki daga ƙasashen Turai da aka keta alfarmar Al-Qur'ani

Kasar Yemen ta haramta shigowa da kayayyaki daga kasashen turai da suka kyale keta alfarmar Al-Qur'ani, a cikin wani mataki wanda shugaban fafutika ta Ansarullah a kasar ya bayyana da "takunkumin tattalin arzuki."

A cikin wata tattaunawa wadda shugaban majalisar siyasa a Yemen, Mahdi al-Mashat, ya jagoranta a ranar Asabar a birnin Sana'a, majalisar ta yi Allah wadai da cigaba da yin cin mutunci ga littafin Al-Qur'ani mai tsarki akai-akai, na baya-bayan nan wanda shine kona littafin mai tsarki a kasar Denmark kamar yadda kafar watsa labaru ta Saba news agency ta bayyana.

Majalisar "ta umarci gwamnati da ta hana shigowa da kayayyaki daga kasashen da suka kyale yin cin mutunci ga Al-Qur'ani mai tsarki, ta kuma shirya yadda za a tabbatar da hakan." 

Da safiyar ranar Juma'a, shugaban kungiyar fafutika ta Ansarullah a Yemen, Seyed Abdul-Malik al-Houthi, ya yi kakkausar suka da Allah wadai da laifin kona Al-Qur'ani mai tsarki a kasashen turai, inda ya nemi musulmai da su dauki matsaya a kan yaki da ake yi a kan musulunci.

"Son mu da addini ya bukaci mu nuna bacin ran mu, mu nuna damuwa a lokacin da suka fara yaki da addininmu." Ya bayyana.

Da ya ke bayyana yadda kasashen yamma ke son abubuwan da suka shafi duniya, al-Houthi ya bayyana cewa ya kamata kasashen musulmai su tunkare su da makaman takunkumin tattalin arzuki.

"Mu, a matsayinmu na musulmai, ya kamata mu sa takunkumi ga duk kasashen da suka kyale kona Al-Qur'ani kuma a doka suka goyi bayan hakan, domin takunkumin ya isa ya sa makiyan su dakata su kuma tursasasu daina cin mutuncin musulunci." Kamar yadda al-Houthi ya bayyana.

Yawan yadda ake cin mutuncin musulunci da littafin Al-Qur'ani mai tsarki na kara hauhawa a kasashen turai.

Kasashen turai da dama na kyale wannan mummunan al'amari faruwa a kasashensu, kuma keta alfarmar Al-Qur'ani da akan yi kan jawo yin Allah wadai daga kowanne bangare na kasashen musulmai da ke duniya.

A cikin satin da ya gabata, mambobin wata kungiya a kasar Denmark, Patrioterne Gar Live, sun taru a harabar ofishin jakadancin Turkiyya da ke Copenhagen, ruke da rubuce-rubucen da ke cin mutuncin musulunci inda suka kona kwafin Al-Qur'ani da kuma tutar kasar Turkiyya, kuma suka sa bidiyon hakan na faruwa a shafinsu na kafar sada zumunta ta Facebook.

Kasashen Turkiyya, Iran, Qatar, Saudi Arabiya, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Jordan, Morocco da Pakistan sun yi Allah wadai da wannan al'amari wanda ya cutar da biliyoyin musulmai da ke fadin duniya.

No comments

Powered by Blogger.