Header Ads

'Yan ta'adda sun sace mata 2, ɗaliban jami'ar gwamnatin Tarayya da ke Gusau

Alamin Jami'ar Tarayya da ke Gusau

'Yan ta'adda sun sace wasu 'yan mata biyu daluban Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, jihar Zamfara, bayan sun kai hari a dakin kwanan daluban da ke waje da makarantar a wani yanki da ake kira Sabon Gida a cikin babban birnin jihar a ranar Lahadi.

Kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito, daluban guda biyu, Maryam da Zainab, an sace su ne wajen karfe 01:42 na dare.

Maryam da Zainab dai dalubai ne da ke karantar Microbiology a jami'a, kuma suna cikin dakinsu ne a lokacin da 'yan ta'addan suka kawo hari a yankin.

Hukumar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da sace su din da aka yi, kuma ta bayyana cewa ana kokari wajen ganin an ceto su.

Mohammed Shehu, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sanda a jihar, Yusuf Kolo, ya bayar da umarnin hada wata kungiya wadda aka shirya a tsanake domin ceto daluban.

"Bayanin da muke samu na nuna cewa a ranar 2 ga watan Afirilun 2023 da karfe 0100 na dare, wasu 'yan bindiga sun afka cikin kauyen Sabon Gida da ke karamar hukumar Bungudu tare da shiga cikin dakunan kwanan daluban jami'a inda suka kulle masu gadi guda biyu tare da kwace wayoyin hannun su, daga bisani kuma suka sace dalubai mata guda biyu masu karantar Microbiology a jami'a." Kamar yadda Malam Shehu ya bayyana, inda ya kara da cewa hukumar ta samar da karin jami'an tsaro domin su taimaka wajen cigaba da neman daluban da ake yi.

Ayyukan ta'addanci na shafar dalubai a jihar Zamfara da sauran jihohin arewacin Nijeriya tun cikin shekarar 2014 a lokacin da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata sama da 200 a Chibok da ke jihar Borno.

Tun daga wannan lokaci, 'yan ta'adda wadanda akan kira su da 'yan bindiga a arewa-maso-yammaci suka runka kai hare-hare a makarantu tare da sace dalubai, musamman a Makarantar Sakandiren Kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara jihar Neja, Makarantar Sakandiren 'Yan mata da ke Jangebe a jihar Zamfara, Kwalejin Aikin Gona da Kimiyyar Dabbobi da ke Bakura, jihar Zamfara, Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yauri jihar Kebbi, Greenfield University da ke jihar Kaduna da sauransu.

No comments

Powered by Blogger.