Header Ads

'Yan sanda sun kai hari ga masu zanga-zanga a Faransa bayan zartar da dokar fansho

Jami'an tsaron Faransa na musgunawa masu zanga-zanga 

Jami'an 'yan sanda a kasar Faransa sun kai hari ga masu gudanar da zanga-zanga a Rennes kwana daya bayan shugaban kasar, Emmanuel Macron, ya sa hannu domin tabbatar da dokar karin shekaru biyu a kan shekarun da mutum zai yi ritaya a kasar, wanda hakan ke nuna ya yi watsi da zanga-zangar da aka share wata biyu ana yi tare da kiraye-kirayen kada ya tabbatar da dokar.

An dai ga 'yan sanda na amfani da karfi kan masu zanga-zangar a ranar Asabar, inda suke fesa ruwa, barkonon tsohuwa (tear gas) tare da amfani da karfi domin killacewa da kama mutane domin dai kawai su watsa taron jama'a.

Bangaren masu zanga-zangar sun tsaya ne a bayan lemomi da katakai domin kare kansu daga ruwan da ake fesowa, wanda hakan ke nuna cewa ba su hakura da abinda suke nema ba.

"Akwai matar da ta fadi kasa kuma ake jan ta, sai kuma wani mutum ya zo domin ya taimaka mata da kuma yadda ake yi masa godiya... Ku (hukumomi) kun ji kunya... Yin amfani da karfin da ya fi kima, wannan daidai ne?" Wani mai zanga-zanga aka bayyana na cewa.

Da safiyar ranar ne dai wadanda ke zanga-zangar masu yawan gaske suka shiga cikin birnin domin gudanar da zanga-zangar wadda kungiyoyin ma'aikata da kungiyoyin hadin gwiwa suka kira da a yi.

"Hanya daya da za a iya dawo da daidaituwar al'amurra shine a janye dokar. Wannan wani aiki ne na cin mutunci ga ma'aikatan da ke kasar." Cewar wani wakilin kungiyar Force Ouvriere union ya bayyana.

"Abinda muke dauke da shi a zuciyarmu, gabbanmu da jijiyoyinmu shine sabuwar makoma, daidaito, 'yan uwantaka a cikin al'umma da adalci a tattalin arzuki. Wannan shi mu ke yi a yau." Kamar yadda ya bayyana.

Zanga-zangar dai ta barke ne tun cikin watan Janairu bayan da gwamnatin ta yi yunkurin haifar da canje-canje ba tare da ganin an gudanar da zabe kan hakan a majalisar kasar ba.

Bayan gudanar da zanga-zanga ta tsawon watanni a duka fadin kasar kan yunkurinsa na kara shekarun aiki kafin a yi ritaya, a ranar Asabar Macron ya sa hannu domin kudurin ya zama doka, wannan kuwa ya kara fusata kungiyoyin ma'aikata inda suka yi kira da a cigaba da zanga-zangar.

Dokar wadda za a tabbatar a ranar 1 ga watan Satumba, za ta kara yawan shekarun da ma'aikata za su yi suna aiki ne kafin samun fansho daga 62 zuwa 64.

No comments

Powered by Blogger.