'Yan sanda sun bindige 'yan bindiga biyu a jihar Zamfara
Wasu 'yan bindiga biyu sun rasa ransu yayin harbe-harben bindiga tsakaninsu da jami'an 'yan sanda a cikin wani gari a karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.
Sauran 'yan bindigan wadanda ke da harsasai a jikinsu sun gudu, kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar Zamfara, CSP Muhammad Shehu, ya bayyana a cikin wani jawabi a ranar Litinin.
"'An dakile harin da 'yan bindigan suka yi niyyar kaiwa ga al'umma, inda biyu daga cikinsu suka rasa ransu sauran kuma suka gudu kuma ana kyautata zaton suna da harbin bindiga a jikinsu." Kakakin 'yan sandan ya bayyana.
Ya ma kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, Mista Kolo Yusuf, ya yaba da kokarin jami'an 'yan sandan.
Ya tabbatarwa mazaunan yankin cewa rundunar ta 'yan sanda ta mayar da hankalinta wajen dakile duk wasu ayyuka na batagari a fadin jihar.
"Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana godiyarsa ga kokarin da 'yan sanda da kuma sojoji ke yi a jihar wajen ganin sun kawo karshen ayyukan 'yan bindiga da kuma sauran ayyukan ta'adda." Kamar yadda ya bayyana, inda ya yi kira ga duka sauran 'yan kasa da su cigaba da nuna goyon bayansu ga jami'an tsaro a kokarin da suke yi na tabbatar da zaman lafiya da dawwamammen tsaro a jihar.
Ya bayyana cewa rundunar za ta cigaba da samun cigaba da kuma fada da 'yan ta'adda a jihar.
Post a Comment