'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda 5 da wani mutum da matarsa a jihar Imo
'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyar a Ulakwo da ke karamar hukumar Ngor Okpala a jihar Imo da ke Kudu-maso-gabashin Nijeriya.
Al'amarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Juma'a kamar yadda PREMIUM TIMES ta ruwaito.
Majiyoyi sun shaidawa jaridar cewa jami'an na 'yan sanda sun tuka motarsu ne daga wani wuri da ke karamar hukumar Abor Mbaise inda daga bisani suka tsaya a Ngor Okpala domin su ci abinci a wani karamin shagon cin abinci.
'Yan bindigan, kamar yadda aka bayyana, sai suka tuka motarsu zuwa yankin tare da bude wuta kan jami'an 'yan sandan, kuma nan take suka kashe uku daga cikinsu.
Biyu daga cikin 'yan sandan wadanda suka samu raunuka sai suka ruga wani shago da ke kusa domin su tsira da ransu, inda kuma 'yan bindigan suka binciko su tare da kashe su.
Bayan jami'an da 'yan bindigan suka kashe, wani mutum da matarsa ma da ke cikin shagon 'yan bindigan sun kashe su. Mutanen an bayyana sunansu da Mista da Misis Chinaka Nwagu.
"'Yan bindigan sun tafi da bindigogin 'yan sandan bayan kashe su." Kamar yadda Onyebuchi Okpara, wani mazaunin yankin, ya shaidawa jaridar.
A yayin da aka tuntube shi, kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar al'amarin kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito.
"A yanzu haka da na ke magana da ku, muna gudanar da babban sintiri a Ngor Okpala da niyyar kamo wadanda suka yi wannan mummunar aika-aika domin su fuskanci hukunci." Kamar yadda kakakin ya bayyana.
Kakakin ya bayyana cewa 'yan bindigan sukan kai hari sannan nan da nan su koma maboyarsu domin kada jami'an tsaro su kama su.
"Amma yanzu za mu kai yakin ne har inda suke. Za mu nemo su a inda suke." Kamar yadda Mista Okoye ya tabbatar.
Kamar sauran jihohi a kudu-maso-gabashin Nijeriya, tsaro a jihar Imo ya lalace inda 'yan bindiga kan kai hare-hare akai-akai.
Hare-haren an fi kai su a kan jami'an tsaro, jami'an gwamnati da sauran kayayyaki.
Gwamnatin Nijeriya na zargin kungiyar fafutikar kafa kasar Biyafara (IPOB) da kai hare-hare a yankin, sai dai kungiyar ta sha musanta hannu a cikin hare-haren.
IPOB dai kungiya ce da ke fafutikar kafa kasar Biyafara, kuma ta na son cire kasar ne daga kudu-maso-gabashi da kuma wani bangaren kudu-maso-kudu a Nijeriya.
Post a Comment