Header Ads

Yahudawan Isra'ila na so su yanka dabbar sadaukarwa a masallacin Kudus yayin bikin Yahudawa na Passover.

Wani dan sandan Isra'ila na samar da kariya a yayin da wasu Yahudawan Isra'ila suka kutsa cikin harabar masallacin al-Aqsa

Yahudawan Isra'ila sun sake yin kira da a kyale su su yanka dabba a harabar masallacin al - Aqsa a gabashin al-Quds da aka mamaye a yayin wani biki na Yahudawa duk da nuna kin amincewa da hakan daga bangaren al'ummar Musulmai da kuma yiwuwar arangama da Falasdinawa. 

Kiraye-kirayen an yi su ne a cikin wata wasika wadda wasu malaman Yahudawa 15 suka sawa hannu zuwa ga firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da kuma minista mai bayar da shawara a kan tsaro, Itamar Ben-Gvir, a ranar Alhamis a yayin da bikin na Yahudawa, Passover, za a yi shi ne a ranar 5 ga watan Afirilu kuma a wannan shekarar ya kama cikin watan Ramadan. 

Wannan kuwa na zuwa ne duk da cewa masallacin al - Aqsa - wanda shine masallaci mafi daraja na uku a Musulunci - an haramta yin duk wata bauta ko al'amari wanda ba na Musulunci ba a tsawon shekaru da dama a karkashin yarjejeniyar kasa-da-kasa.

Wasu kungiyoyi a Isra'ila akai-akai su kan yi kira da a bari a yi yankan sadaukarwa da dabba a wannan haraba mai tsarki, wadda 'yan Isra'ilan ke kira da Temple Mount.

A yayin da majalisar Isra'ila da dadewa tana kin sauraron wadannan kiraye-kiraye domin gudun yadda al'ummar Musulmai na duniya za su mayar da martani kan al'amarin da kuma mutanen Falasdinawa, wasu sannannu a cikin majalisar ta Isra'ila na goyon bayan yin bautar Yahudawa a harabar. 

A cikin watan Janairu, Ben-Gvir ya shiga harabar masallacin al-Aqsa mai tsarki ta kofar Moroccan Gate, wadda aka fi sani da Mughrabi Gate, a wani yanayi na keta alfarmar wajen, hakan kuwa ya haifar da martani daga Falasdinawa wadanda suka bayyana hakan da "Wani tonan fada wanda ba a taba yin sa a baya ba."

Afkowar Yahudawan Isra'ila cikin masallacin al - Aqsa ya karu sosai tun bayan fara mulkin da Benjamin Netanyahu ke jagoranta.

Irin wannan kutsowa ta Yahudawan Isra'ilan kusan a kodayaushe kan faru ne a karkashin umarnin kungiyoyin da ke samun goyon bayan Tel-Aviv da goyon bayan 'yan sandan Isra'ila da ke al - Quds, wanda hakan ke haifar da arangama da Falasdinawa a masallacin, inda ake raunata wasu, a kame wasu, a kashe wasu.

Wannan abu ya kasance wani babban al'amari a tsakanin Isra'ila da ke mamaya da kuma Falasdinawa. Wannan ya kasance babban al'amari a yayin Intifadar Falasdinawa a shekarun 2000 zuwa 2005, wanda kuma aka san shi ma da yunkurowa.

No comments

Powered by Blogger.