Yadda Al'ummar musulmai suka yi Eid al-Fitr
Miliyoyin al'ummar musulmai a kasashe da dama sun gabatar da bukukuwan Eid al-Fitr a ranar 21 ga watan Afirilun shekarar 2023 wanda ke yin nuni da kammala azumin watan Ramadan mai alfarma bayan ganin sabon watan Shawwal a daren da ya gabata.
Al'ummar musulmi da suka gabatar da ibadar azumi a cikin watan Ramadan sun gabatar da sallar idi a kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar, Jordan, Sudan, Syria, Yankunan Falasdinawa da aka mamaye na Isra'ila, mafiyawancin masarautun yankin tekun fasha, kasashen arewacin Afirka, yammacin Afirka ciki harda Nijeriya da sauransu.
Dubunnan daruruwan musulmai ne suka taru a kasar Saudi Arabiya a birane masu tsarki na Makka da Madina domin gabatar da sallolin Eid al-Fitr da safiyar ranar Juma'a kamar yadda Saudi Press Agency ta ruwaito.
A Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) dubunnan masu gabatar da ibadar ne suka tafi masallatai domin gabatar da sallah a ranar idin kafin daga bisani su gabatar da bukukuwa tare da iyalansu.
"Yau itace ranar Eid al-Fitr." Wani limami a Dubai ya bayyana, "Hakan na nufin farin ciki, yana da muhimmanci a yi farin ciki a ranar Idi kuma a ziyarci iyalai da 'yan uwa."
A yankin da aka mamaye na birnin al-Quds, masu gabatar da ibada mutum 120,000 suka gabatar da sallar idi a masallaci mai tsarki na al-Aqsa duk da tsauraran matakan da Isra'ila ta dauka.
Kamfanin watsa labarun Falasdinawa, Wafa, ya bayyana cewa sojojin Isra'ila sun farmaki matasan Falasdinawa, inda suka rinka dukansu da sanduna a kusa da Lion's Gate a birnin al-Quds da aka mamaye a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa sallar idi.
Musulmai a kasashen Iran da Iraq ana sa ran za su gabatar da sallar idin ne a ranar Asabar.
Post a Comment