Header Ads

Wa'adin 31 ga watan Disamba: Masana sun damu sakamakon rashin wadatattun sabbin kudi

Sabbinnkudin da har yanzu ba su wadatu ba

Mista Gabriel Okeowo, daraktan wata kungiya wadda ba ta gwamnati ba mai suna BudgiT Foundation Nigeria, ya nuna damuwarsa kan rashin wadatattun sabbin kudi.

Mista Okeowo ya bayyana damuwarsa ne a yayin wata tattaunawa da yi da kungiyar dillancin labarun Nijeriya (NAN) a Abuja a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa watanni shida kafin cikar wa'adin tsoffin takardun kudaden, ya kamata babban bankin Nijeriya (CBN) ya samar da isassun sabbin takardun kudin a yayin da kuma a hankali yana janye tsoffin takardun kudaden.

Kamar yadda ya bayyana, idan babban bankin na Nijeriya ya cigaba da sakin tsofaffin kudaden ba sabbin ba, zai yi wahala a iya janye su zuwa wa'adin 31 ga watan Disamba.

Okeowo ya bayyana cewa bayan bukatar da ake da ita na samar da sabbin takardun kudaden, akwai bukatar samar da yanayin yanar gizo mai kyau ga bankuna domin tabbatar da wanzuwar tsarin na rashin kudade a hannu (cashless policy).

"Idan abinda ya ke a yanzu tsoffin takardun kudi ne, hakan na nufin sabbin takardun kudin ba su wadata ba.

"Kuma a yanzu da muke magana, dogayen layukan ba wai sun tafi ba ne baki daya, a kan samu matsaloli yayin gudanar da kasuwanci ta yanar gizo kuma ba a cika dawo da kudade cikin awowi 24 ba a mafi yawancin lokuta.

"Bayan haka, yanayin yanar gizo da ake da shi bai yi cigaban da za a iya yin kasuwanci ta shi ba.

"Idan ba a yi gyara a kan wadannan abubuwa ba, ina hangen kara wa'adi bayan wa'adin 31 ga watan Disamba." Kamar yadda ya bayyana.

A dai ranar 3 ga watan Maci ne kotun kolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa tsoffin takardun kudi na N1000, N500 da N200 su cigaba da kasancewa a matsayinsu na takardun kudi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Wannan hukunci kuwa ya biyo bayan wahalhalun da 'yan Nijeriya suka shiga ne biyo bayan canza fasalin kudin da kuma tsarin rashin takardun kudade a hannu (cashless policy) na CBN wanda aka fara daga ranar 31 ga watan Janairu.

No comments

Powered by Blogger.