Header Ads

Sudan: Motocin bas 40 sun kwashe daliban Nijeriya 2,400 zuwa Cairo da ke Misra

Wasu 'yan
Gwamnatin tarayya ta samar da motocin bas 40 domin fitar da daluban Nijeriya da ba su gaza 2,400 ba wajen Sudan a yau. 

Shugabar hukumar 'yan Nijeriya da ke kasar waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ce ta tabbatar da haka a daren jiya.

Kamar yadda ta shaidawa jaridar The Nation, Dabiri-Erewa ta bayyana cewa motocin za su tashi ne daga garin kan iyaka na Luxol da Aswan zuwa Cairo, wato babban birnin kasar Misra, daga nan kuma Air Peace zai kwaso su zuwa Nijeriya.

Daga dai Luxol zuwa Cairo kusan awa takwas ne a kan hanya a yayin da kuma daga Aswan zuwa Cairo kusan awa 11 ne.

Gwamnatin ta gargadi wadanda suka rage a Sudan din da kada su kuskura su yi wata tafiya mai hadari zuwa kan iyaka.

Ta ma nemi wadanda abin ya shafa da kada su tayar da hankulansu kuma su kasance suna magana da ofishin jakadanci akai-akai. 

Akalla dai mutane 459 ne suka rasu kawo yanzu a sakamakon yakin, kodayake hakikanin adadin ana tunanin ya fi haka.

Duka dai bangarorin biyu da ke fada da juna sun amince su tsagaita wuta.

Ana kallon rahoton tsagaita wutar a matsayin abinda zai tseratar da rayukan fararen hula wadanda suka kasa fitowa daga cikin gidajensu kuma ba tare da samun dama ta samun abinci, tsaftataccen ruwan sha da kiwon lafiya ba.

No comments

Powered by Blogger.