Sowore ya yi watsi da neman gafarar da Buhari ya yi tare da zarginsa da daukar 'yan Nijeriya kamar ba mutane ba
Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, da dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore
Dan takarar kujerar shugaban kasa a Nijeriya a karkashin jam'iyyar African Action Congress (AAC) a babban zaben da ya gabata na shekarar 2023, Omoyele Sowore, ya yi watsi da neman gafarar shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya yi ga 'yan Nijeriya a yayin da wa'adin mulkinsa ke zuwa karshe.
Sowore ya bayyana rashin gamsuwarsa ne da neman gafarar da Buhari ya yi a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana dalilai da za su iya sawa ba za a yafewa Buhari ba saboda wasu abubuwa da ya aikata.
A dai ranar Juma'a ne Buhari ya roki 'yan Nijeriya su yafe masa, musamman wadanda ya bata ma wa a yayin gudanar da ayyukansa.
To sai dai Sowore bai biyewa kalaman shugaban kasar ba, inda ya bayyana cewa Buhari ba wai kawai ya bata wa 'yan Nijeriya bane, amma ya ma dauke su kamar ba mutane ba ta hanyar tsare-tsaren sa wadanda ba su yi kyau ba.
Sowore ya cigaba da lisasafo ayyukan Buhari wadanda ba su yiwa kasa kyau ba.
Sowore ya bayyana cewa, "Ka hana 'yan Nijeriya rayuwa mai kyau, ka hana yara, mata, maza - tsofaffi da matasa - damar su yi rayuwa su habaka. Ka rugurguza kasuwanci, ka kashe rayukan da ba su da laifi, ka rugurguza bangaren ilimi, ka hana marasa lafiya da masu nakasa damar kulawa da su domin lafiyarsu."
Dan takarar shugaban kasar ya ma zargi Buhari da tsarewa tare da kulle 'yan Nijeriya da dama ba tare da hakki ba, rurura rigima tare da haifar da rarraba ta hanyar addini da kabilanci.
Sowore ya ma kara da zargin shugaban kasar da 'yan amshin shatansa da cewa sun aikata cin hanci ba karami ba a lokacin da suke ofis.
Dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa damammakin da Buhari ya hana "zasu cigaba da bibiyarsa" har zuwa karshen lokaci.
A bayyana ya ke dai cewa Sowore bai gamsu da neman gafarar da shugaban kasar ya yi ba, kuma ya yi imanin cewa abubuwan da ya aikata a lokacin da ya ke kan mulki za su kasance masu shafar 'yan Nijeriya na lokaci mai tsawo.
Post a Comment