Sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasdine tare da raunata wasu 3
Sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasdine tare da raunata wasu uku a yayin wani hari da suka kai a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Ariha a gabashin yamma da gabar kogin Jordan a yayin da zaman dar-dar ke kara hauhawa a yankunan da aka mamaye.
Gwamnan Ariha da Jordan Valley, Jihad Abu al-Asal, ya shaidawa kafar watsa labarun Falasdinawa ta Wafa cewa mutumin, wanda aka bayyana sunansa da Suleiman Ayesh mai shekara 20, an yi masa mummunan harbi a sansanin 'yan gudun hijira na Aqabat Jaber a ranar Litinin.
Gwamnan ya kara da cewa majiyoyin lafiya na Falasdinawa sun bayyana cewa mutane uku suma sun raunata sakamakon harbe-harbe ba tare da kula ba da sojojin na Isra'ila suka yi a sansanin.
Sojojin na Isra'ila sun bayyana cewa suna aiki ne a wurin sai suka ga wasu wadanda ake zargi biyu suna gudu. Sai sojoji suka bude masu wuta inda suka samu akalla daya daga ciki.
A cikin watannin da suka gabata Isra'ila ta kara yawan kai hare-haren da ta ke kaiwa a garuruwa da biranen Falasdinawa a yankunan da aka mamaye. A sakamakon haka Falasdinawa da yawa sun rasa rayukansu wasu kuma an kama su.
Tun fara azumin watan Ramadan, gwamnatin Isra'ila ta sanya tsauraran matakai a hanyoyin shiga da fitar Falasdinawa a kofofin masallacin al-Aqsa.
Ko a ranar 4 ga watan Afirilu, sojojin Isra'ila sun afka harabar masallacin al-Aqsa kafin daga bisani su fara harba hayaki mai sa hawaye (tear gas) da gurneti a wurin da ake sallah inda daruruwan maza, mata, dattijan mutane da yara ke gabatar da sallah a tsawon dare. Wasu wadanda suke shaidun gani da ido ma sun bayyana cewa har harsasai an harba.
Post a Comment