Soja ya harbe wani dan sanda a jihar Borno bayan kama motar wani soja da tabar wiwi
Wani soja da ke da hannu a cikin dakon wiwi da dan uwansa soja ya yi ya budewa wani jami'in dan sanda wuta bayan kama motar da aka yi dakon wiwi din da jami'an 'yan sanda suka yi a jihar Borno.
Wannan al'amari ya afku ne bayan jami'an 'yan sanda a garin Benishek da ke jihar Borno sun kama wani sojan Nijeriya, Sajent Undei Josept, mai lambar aikin rundunar soja 02/NA/52/3510, wanda ya yi dakon tabar wiwi daga garinsu bayan hutun aikinsa ya kare a cikin motarsa kirar Acura Jeep mai lamba Lagos FKJ76 tare da isowa garin na Benishek da ita.
Jami'an 'yan sandan sun kama sojan ne a cikin motar yayin da suke duba ababen hawa inda kuma ya ki tsayawa, su kuma ganin haka suka fasa tayar motarsa da harsashi.
Bayan jami'an 'yan sandan sun kama sojan sai wani dan sanda ya shiga motar domin karasawa da ita ofishin 'yan sanda da ke Benishek, inda wani soja da ke da hannu a cikin dakon tabar wiwi din ya budewa dan sandan wuta ya kashe shi.
A yanzu haka dai rundunar sojin Nijeriya ta kama jami'in sojan da ya yi dakon wiwi din da kuma jami'in sojan da ya yi harbin, inda kuma a cikin rahoton da ta fitar ta bayyana cewa harbin bisa kuskure ne.
Dan sandan da sojan ya harbe musulmi ne mai suna Sajen Ahmad Ali, Allah Ya gafarta masa ya kai rahama a kabarinsa.
Post a Comment