Shugaban hukumar leken asirin Amurka na cikin damuwa sakamakon sake kulla dangantaka tsakanin Iran da Saudiyya
Shugaban hukumar leken asirin Amurka ta CIA, Williams Burns, ya nuna damuwarsa ga mahukuntan kasar Saudiyya sakamakon daidaita dangantaka a tsakanin masarautar da kasar Iran wanda kasar Sin ta jagoranta a cikin watan Maci, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaidawa jaridar Wall Street Journal.
Burns ya shaidawa hukumomin Saudiyya cewa yarda da Saudiyya ta yi ta daidaita dangantaka da Iran wani abu ne wanda Amurka ba ta yi tunanin faruwarsa a yanzu ba.
A yayin wata tafiya da ya yi cikin satin nan wadda ba a bayyana ta ba, Burns ya shaidawa hukumomin Saudiyya cewa Washington na "fuskantar wani hadari wanda ba ta iya ganinsa da kyau" a kan yadda za ta sabunta diflomasiyyarta da kasar Iran da Syria, kamar yadda majiyoyi da dama su ka shaidawa Journal a ranar Alhamis.
Ministocin Harkokin Kasashen Wajen Iran da Saudiyya sun tattauna a birnin kasar Sin a ranar Alhamis. Sun kuma fitar da jawabi wanda ya shafi abubuwa da dama wadanda suka hada da bude ofisoshin jakadancinsu da sauran ofisoshin kasa-da-kasa na kasashen biyu, bayyana sunayen ambasadoji da ma kuma ziyarar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi, birnin Riyadh.
Zuwa ranar Alhamis, 6 ga watan Afirilu, dangantakar diflomasiyya a tsakanin Iran da Saudiyya ta dawo a hukumance.
A yayin da ya ke jawabi ga manema labaru a ranar Alhamis a Beijing, kakakin Ma'aikatar Kasashen Wajen kasar Iran, Nasser Kanaani, ya yaba da "kyakkyawar tattaunawa" da aka yi a tsakanin ministocin kasashen wajen kasar Iran da Saudiyya. Ya bayyana cewa an yi tattaunawar "a wani yanayi mai kyau."
Kanaani ya bayyana cewa domin yin shirye-shiryen bude ofisoshin jakadanci a Tehran da Riyadh da kuma sauran ofisoshin kasa-da-kasa a tsakaninsu, kasashen musulman biyu za su tura da wakilai kwararru a tsakaninsu a cikin kwanaki masu zuwa.
Bayan tattaunawarsu mai cike da tarihi ta ranar Alhamis a Beijing, Ministocin Harkokin Kasashen Wajen Iran da Saudiyya din sun fitar da jawabi na hadaka.
Post a Comment