Header Ads

Shekaru bakwai bayan kisan kiyashin Zariya, an ba 'yan'uwa musulmi ababen hawansu

Wani bangare na motocin da aka mayarwa almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky

Biyo bayan umarnin wata babbar kotu a Kaduna, a ranar Asabar, 1 ga watan Afirilun wannan shekara ta 2023, ne aka ba 'yan Shi'a almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky, ababen hawansu da aka damkawa 'yan sanda a shekarar 2015, wato shekaru bakwai kenan bayan kisan kiyashin da aka yi masu a Zariya.

A dai cikin shekarar 2015 ne wasu sojojin Nijeriya suka dira kan 'yan Shi'ar da kisa biyo bayan zarginsu da tarewa shugaban hafsan sojojin kasa na Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Burutai, hanya.

Wannan lamari kuwa ya haifar da rasa rayuka da dukiyoyi da dama, inda gwamnatin jihar Kaduna ta yi ikirarin mutane 347 ne aka yiwa kabarin bai daya, saidai bangaren almajiran shehin malamin sun musanta hakan, inda suka ce adadin wadanda suka rasa rayukansu sun fi karfin dubu daya.

Su ma kungiyoyin kare hakkin bil-adama, Amnesty International da Human Rights Watch duk sun bayyana cewa yawan wadanda suka rasa rayukansu sun fi yawan da gwamnati ta bayyana.

Ababen hawan wadanda aka bayar bayan afkuwar wannan al'amari da shekara bakwai, kamar yadda lauyan da ya tsayawa almajiran shehin malamin a kotu, Barista M. Abu, ya bayyana ba su kai yawan wadanda aka shigar kara a kotu ba, domin a cewarsa, ababen hawa 67 ne ke kasa.

Ababen hawan dai sun hada da kananan motoci, babura, keke napep da motar asibiti. Kuma wasu motocin da yawansu an farfasasu da harsasai. Wasu ababen hawan da aka damkawa 'yan sandan an sace tayoyinsu, injinansu, rima-rimansu, batiransu da sauransu.

Baristan da ya tsayawa almajiran shehin malamin a kotu a cikin bayanin da yi ga manema labaru ya bayyana cewa tun cikin shekarar 2022, mai shari'a A.A. Amina ta bayar da umarnin bayar da ababen hawan, inda ya bayyana cewa, "Adadin ababen hawan da muka shigar da kara a kai ya zarce adadin da muka gani a yanzu a nan. Adadin ababen hawan da ke yanzu a nan 67 ne kawai kuma ya kamata a ce sun fi haka." Inda ya bayyana cewa wadanda suke a nan din ma duk an lalata su kuma bai kamata a same su a haka ba, inda a cikin jawabin da ya gabatar din ya bayyana cewa za su duba matakin da za su dauka a nan gaba saboda ababen hawan da aka ba su ba su kai yawan wadanda suka shigar kara ba.

Kamar yadda lauyan ya bayyana, bayan abinda ya faru a tsakanin 'yan shi'a da sojoji a cikin shekarar 2015, an kama daruruwan 'yan Shi'a da ababen hawansu bisa zargin tare hanya, kuma mafi yawa a gefen hanya da gidan malaminsu ne aka kwashe su. Inda sojoji suka kwace masu ababen hawansu tare da kama mutane da yawa wadanda suka mikawa 'yan sanda domin gudanar da bincike da gurfanar da su da domin yanke masu hukunci. 

Barista M. Abu ya bayyana cewa an tafka shari'a inda wadanda aka gurfanar da su din aka sake su tare da wanke su daga dukkan zarge-zarge.

Saidai a cewarsa, a bangaren ababen hawansu ba a taba gabatar da su a gaban kotu ba. Hakan ta sa aka shigar da kara a gaban kotu domin ganin an bayar da ababen hawan, kuma hukuncin da kotun ta yanke ne ya sa suka kasance a wannan ofishin 'yan sanda na MTD da ke karamar hukumar Sabon Gari Zariya domin karbar ababane hawan.  

A yayin da shima ya ke tattaunawa da manema labaru, daya daga cikin wadanda suka zo karbar ababen hawansu mazunin Kaduna mai suna Sidi Muhammad Balarabe Ma'azu Kadaure Kaduna, ya bayyana cewa da yawa kayayyakin kamar yadda suka zo suka same su an ciccire abubuwan da ke cikin babura da motocin. An cire injinansu, inda ya bayyana cewa sai dai ka dauki gwamgwanin mota ko babur, kuma kamar shi an cire tayoyin babur dinsa ne ma.

Sidi Muhammad, wanda ya bayyana cewa an basu wasu takardu domin su cika kafin daukar kayayyakin nasu, a cikin jawabin nasa ya bayyana cewa, "Dukkaninmu 'yan uwa sai dai mu yi ta cewa alhamdulillahi, mun godewa Allah. Mun samu wani abinda a ranar gobe Kiyama mun samu wani abinda zai zamo mana shaida ne game da al'amurran da muka ba da gudummuwa mu a namu jinanen, da dukiyarmu da komai da komai. Kar ka sa ma kan ka damuwa, wannan abu da ya zo ya faru ka dauke shi a matsayin kaddara kuma rubutaccen abu Allah ne ya ga dama ya yi amfani da shi wajen isar da wannan sakon." Inda ya bayyana cewa a wannan kira da Malam Zakzaky ke yi kowa na da aikin da ya ke yi a kai tare da kira da cewa kowa ya kara kaimi a kan aikin da ya ke yi kada ka yarda ka yi abinda ya sabawa harka ko ayi wani abu da kai wanda zai kasance abin zargi ga harkar musulunci. 


Kamar yadda wani wanda ya bibiyi tabbatar da ganin an bayar da ababen hawan ya bayyana mai suna Ado Sahifa, sun karbi motoci 67, babura 10 da keke napep 3.

Wakilinmu wanda ya ke daya daga cikin manema labaru da ya halarci wajen ya ga almajiran shehin malamin da dama da suka zo wannan ofishin 'yan sanda wajen karbar ababen hawan.

No comments

Powered by Blogger.