Header Ads

Shaguna sama da 200 sun kone sakamakon ibtila'in gobara a wata kasuwa a garin Fatakwal

Gobarar sa'ilin da take ciki

Shaguna da ke dauke da kaya na miliyoyin naira sun kama da wuta a wata sananniyar kasuwa mai suna Ojoto Market da ke Azikiwe/Ojoto roundabout a Mile 2 Diobu da ke Fatakwal a cikin daren ranar Alhamis.

An dai bayyana cewa wutar ta tashi ne bayan da aka kulle kasuwar a yayin da kuma 'yan kasuwar kuma duk sun tafi gidajensu.

A yayin da ya ke jawabi game da al'amarin, shugaban kungiyar cigaban kasuwar, Sir Arinze Akupue, a cikin wata tattaunawar wayar tarho, ya bayyana cewa yana gidansa inda wajen karfe goma saura minti biyar na dare sai jami'an tsaro da ke kula da kasuwar suka kira shi cewa ga shi an ga wuta na fitowa daga cikin kasuwar. 

Shugaban cigaban kasuwar ya bayyana cewa ya kira wasu mutane domin su taimaka su kashe wutar kasuwar a yayin da shi kuma ya tuka mota zuwa ofishin hukumar kashe gobara ta jihar domin neman taimakonsu.

Sai dai a ofishin kashe gobara na jihar an ba shi shawarar cewa sai dai ya je Sakatariyar Gwamnatin Tarayya ya fadawa ofishin kashe gobara na kasa domin su ba za su iya taimakonsa ba.

Mista Akupue ya bayyana cewa ya tuka motar sa zuwa Sakatariyar Gwamnatin Tarayya inda ya shaidawa hukumar kashe gobara ta kasa da kuma shugaban su, inda kuma suka biyo sa zuwa wurin da al'amarin ya faru.

Shugaban cigaban kasuwar ya bayyana cewa kusan kashi 85 cikin 100 na shagunan kasuwar sun kone kafin zuwan jami'an hukumar kashe wutar.

Ya ma bayyana cewa wasu batagari sun kai hari ga jami'an hukumar kashe gobarar domin su haifar da rudani su samu damar kwasar kayayyaki.

Kamar yadda ya bayyana, sai da 'yan sandan Azikiwe Police Divisional Headquarters suka kawo dauki ga jami'an hukumar kashe gobarar, a yayin da wutar ta kona kasuwar baki dayan ta.

Ya bayyana cewa sama da shaguna 200 suka kone ba tare da masu shagunan sun iya daukar wani abu daga cikinsu ba, inda ya bayyana cewa shima shagunansa guda uku sun kone ba tare da ya iya cire wani abu daga cikinsu ba. 

Mista Akupue yi watsi da ikirarin da wasu ke yi cewa masu girke-girke ne a kasuwar ke da alhakin tayar da gobarar.

Sai shugaban kasuwar ya yi kira ga gwamnatij jihar da ta kawo taimako da agaji ga wadanda ibtila'in ya shafa.

Kamar yadda wakilin jaridar PM News ya ruwaito, hukumar kashe gobarar jihar Ribas ba su kai dauki yayin annobar gobara saboda ko dai rashin motoci masu kyau ko rashin isassun kudi.

No comments

Powered by Blogger.