Header Ads

Sace kudin mai dalar Amurka biliyan 2.4: Majalisar wakilai ta gayyato Minister Kudi, Sakataren Gwamnatin Tarayya, NNPC da wasu

Zauren Majalisar wakilai ta Nijeriya a Abuja

Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai ta Kasa a kan satar man fetur ya gayyato wasu manyan jami'an Gwamnatin Tarayya a kan binciken da ya ke yi kan ikirarin sace kudin shiga sama da dalar Amurka biliyan 2.4 wanda aka yi daga sayar da gangunan man fetur miliyan 48 ba bisa ka'ida ba a shekarar 2015.

Wasu daga cikin manyan jami'an da aka kira a ranar Talata domin su amsa tambayoyi sun hada da Ministar Kudi, Zainab Ahmed da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha kamar yadda Channels Television ta ruwaito.

Cikin wadanda aka kirawo din sun hada da Akanta Janar na yanzu, Sylva Okolieaboh, kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) da sauransu.

Har wa yau kwamitin ya damu da banbancin alkaluma na kudin da aka sayar da mai a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2014 kuma yana zargin Ministar Kudi da yarda da a biya kudi ga mutanen da ya kamata su yi magana in sun ga ana yin ba daidai ba, ba kamar yadda ya kamata su kasance ba a tsarinsu.

Kwamitin majalisar na wucin gadi na yin bincike ne cikin ikirarin da wadanda ke magana in sun ga an aikata ba daidai ba ne (Whistle-blowers), na cewa an sayar da gangar mai miliyan 48 ba kan ka'ida ba a kasar Sin a shekarar 2015 wanda kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 2.4.

A cikin watan Fabrairu, kwamitin ya zargi Antoni Janar na Kasa, Abubakar Malami, da kuma kungiyar 'yan sanda masu binciken masu laifi ta kasa-da-kasa (Interpol) a kan abinda ya kira shishshigi ga binciken da ya ke yi.

Kwamitin ya sa ayar tambaya a kan me zai sa Interpol za su gayyato wadanda ke sa ido kan al'amurra kuma su yi magana in an aikata ba daidai ba a karkashin umarnin Ma'aikatar Shari'a bayan fara binciken kwamitin.

Saidai shugaban hukumar Interpol din a Nijeriya, Garba Umar, ya ce hukumar ta yi aiki ne kawai da umarnin da Akanta Janar na Kasa ya bayar.

Shugaban kwamitin majalisar a kan satar mai, Mark Gbillah, ya bayyana cewa, "Akwai wata kungiya da ake kira Advocacy for Good Governance and Free Nigeria.

"Ita ce ta yi rubutu zuwa ga Antoni Janar tana bayyana masa cewa akwai wata kungiyar kasa-da-kasa ta masu tursasawa mutum ya yi abinda suke so ko su saki wasu bayanai na sirri da suke so su tursasawa manyan jami'an gwamnati.

"Me zai sa Antoni Janar ya bayar da amsa ga kungiyar da be san ta ba? Wannan na nufin cewa Antoni Janar din da kansa ba zai iya tabbatar da sahihancin kowacce kungiya ba."

Kwamitin, saboda rashin gamsuwarsa da bayanan Interpol, sai ya zargi Antoni Janar da yin shishshigi ga binciken majalisar.

Kwamitin ya damu da tsaron lafiyar wadanda suke magana in an yi ba daidai ba kuma ya dage cewa Ma'aikatar Shari'a ta daina bayar da umarni kai tsaye ga Interpol, amma su biyo ta hannun 'yan sanda ne, saboda a doka Interpol kamata ya yi ta amsa bukatun hukumomin tsaro na kasa.

No comments

Powered by Blogger.