Header Ads

Rasha za ta kai makaman Nukiliya kan iyakar ta da Belarus - Ambasadan Rasha a Belarus

Wani makamin nukiliyar Rasha

Ambasan Rasha a kasar Belarus, Boris Gryzlov, ya bayyana cewa Rasha za ta kai makaman ta na Nukiliya kusa da kan iyakar ta da kasar Belarus, inda za su kasance a kusa da kawancen NATO wanda Amurka ke jagoranta fiye da baya.

Kalaman na Gryzlov na zuwa ne bayan shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana a cikin watan Maci cewa Rasha za ta girke makaman ta na Nukiliya a Belarus, wadda ita da Rasha suke a cikin "hadakar kasashe (union state)".

Daga bisani kuma a cikin watan, kasar Belarus ta nuna amincewar ta da ta girke makaman Nukiliyan na Rasha, inda ta bayyana cewa hakan zai nuna cewa kasashen biyu suna a shirye domin kare kan iyakokinsu da 'yancin su.

Sai dai Ambasadan na Rasha bai bayyana ko a wane wuri za a girke su ba, amma ya tabbatar da cewa akwai wata ma'ajiya da za a kammala, kamar yadda Putin ya bayar da umarni, zuwa 1 ga watan Yuni, sai a kai su yammacin Belarus.

Amurka da kasashen yamma da dama sun nuna damuwarsu na yiwuwar kai makaman na Nukiliya kasar Belarus, inda shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya bayyana hakan da "Wani abu wanda ke haifar da damuwa."

Sai dai Putin ya yi musun cewa wannan abun ba zai karya yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya ba (Nonproliferation agreements), inda ya bayyana cewa Amurka na girke makaman ta na Nukiliya a kasashen turai a shekaru da dama da suka gabata.

"Ba wani abun ban mamaki a nan, Amurka na yin haka a tsawon shekaru. Tun da sun girke makamansu na Nukiliya a kasashen da suke kawayensu. " Putin ya bayyana.

Kamar yadda takwaransa na Belarus, Alexander Lukashenko, ya bayyana, Minsk ta shirya sojojin ta su gyara ma'ajiyar makaman mizayel da ke iya zuwa kowacce nahiya a duniya ta Topol inda a nan ne kuma ake harba su a yayin Tarayyar Sobiya, a wani shiri da kasar sa ke yi domin karbar makaman na kasar Rasha.

To amma dai kamar yadda Putin ya bayyana, Rasha za ta gina wuri na musamman domin makamanta a Belarus, ginin kuma za a kammala shi a farkon watan Yuni.

No comments

Powered by Blogger.