Header Ads

Netanyahu ya hana wadanda ba musulmai ba kai ziyara masallacin al-Aqsa har sai bayan watan Ramadan

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu 

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a cikin wani jawabi daga ofishinsa, ya bayyana cewa za a hana duka Yahudawa 'yan kama wuri zauna da sauran wadanda ba musulmai ba ziyartar masallacin al-Aqsa har sai bayan watan Ramadan.

Bayan wata tattaunawa da ya yi da manyan jami'an soja a ranar Talata, Netanyahu, shi da mai ba shi shawara kan harkokin soja, Yoav Gallant da kuma minista mai ba shi shawara kan tsaro, Itamar Ben-Gvir, sun yanke shawarar hana shigar Yahudawa 'yan kama wuri zauna harabar har sai karshen watan Ramadan, wata mai tsarki wanda a cikinsa ne musulmai ke yin azumi.

Wannan matakin, wanda Isra'ila ta dauka a cikin shekaru da dama da suka wuce, ya zo ne bayan daruruwan Yahudawa 'yan kama wuri zauna da masu tsatstsauran ra'ayi sun kutsa cikin masallacin al-Aqsa a ranar Talata a karkashin kariyar jami'an tsaron Isra'ila a yayin da su kuma Falasdinawa aka hana su shiga.

Yahudawa 'yan kama wuri zauna masu tsatstsauran ra'ayi sun kutsa harabar ne cikin kungiya-kungiya karkashin jagorancin malamin Yahudawa mai tsatstsauran ra'ayi kuma tsohon mamba a majalisar Knesset, Yehudah Glick, kamar yadda kafofin watsa labarai na cikin gida suka bayyana.

Kamar yadda kafofin watsa labarun suka bayyana, an kawo jami'an tsaron Isra'ila kafin a kutso cikin harabar da kuma tursasawa ga masu gabatar da ibada. A ranar Litinin, Yahudawa 'yan kama wuri zauna kusan dubu daya suka kutso harabar masallacin tare da kai hari da tursasawa ga Falasdinawa masu gabatar da ibada, tare da daga tutocin Isra'ila ba tare da damuwa da ya musulmai za su ji a ransu ba.

Falasdinawa sun zargi Isra'ila da dagewa wajen ganin sun Yahudantar da gabashin al-Quds inda masallacin al-Aqsa ya ke tare da kawar da alamunsa na larabawa da musulunci.

A dalilin haka ne, mai rubuta matsayar da aka cimmawa a majalisar dinkin duniya, Francesca Albanese, a satin da ya gabata ta bayyana cewa, "Abinda Yahudawa 'yan kama wuri zauna ke son yi shine ko dai su lalata masallacin ko kuma a dole su mayar da shi baki dayansa ko wani bangarensa wurin da Yahudawa ke yin bauta, kamar yadda ya faru ga masallacin Ibrahimi da ke Hebron, wannan wani abu ne mai matukar tayar da hankali ga Falasdinawa." Kamar yadda ta bayyana.

Kutsawa da Yahudawa 'yan kama wuri zauna ke yi masallacin al-Aqsa karkashin kariyar 'yan sanda na kara hauhawa a cikin shekarun nan, inda ake jikkatawa, kashewa tare da kama Falasdinawa masu yawa.

No comments

Powered by Blogger.