Mutane takwas sun rasa rayukansu a wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai kudancin jihar Kaduna
Akalla mutane takwas rahotanni ke nuna cewa sun rasa rayukansu a cikin wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai a Atak'Njei da ke karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.
Harin na bayan nan na zuwa ne 'yan satuka bayan wasu mutane goma sun rasa rayukansu a wani al'amari mai kama da wannan a Langdon da ke karamar hukumar.
A Atak'Njei a nan ne fadar sanannen sarkin Agwatyap ta ke.
Hukumomin 'yan sanda ba su yi magana a kan al'amarin ba, amma shugaban kungiyar cigaban yankin Atyap, Sam Timbuwak, ya bayyanawa gidan talabijin din Channels Television cewa 'yan bindigan sun afka cikin yankin ne daga cikin wani daji da ke kusa da misalin karfe 9:00 na dare tare da fara harbe-harbe a kan gidajen mutane.
Ya bayyana cewa 'yan bindigan sun kai hari ne a kan gidaje biyar inda suka kashe mutane takwas wasu hudu kuma suka jikkata.
Shugaban na Atyap, wanda ya bayyana cewa inda al'amarin ya faru kusa da shingen sojoji ne, ya koka da rashin zuwan sojojin yankin da wuri har sai da maharan suka gama mummunan aikinsu suka tafi.
Sai ya nemi jami'an tsaro da su dage wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata kuma su binciko wadanda ke da alhakin kai hare-hare a yankin kasar Atyap.
Post a Comment