Header Ads

Mutane hudu sun rasu, 20 sun jikkata yayin harbe-harben bindiga a Amerika

Wurin da aka yi harbin 

Mutane hudu sun rasu a yayin da wasu sama da 20 suka jikkata sakamakon harbe-harben bindiga a wajen wani bikin tunawa da ranar haihuwa a Dadeville da ke jihar Alabama a Amurka.

Jami'an tsaro a jihar Alabama sun bayyana cewa an yi bikin tunawa da ranar haihuwar ne kusan da karfe 10:30 na dare.

Kamar yadda Sgt. Jeremy Burkett na jami'an tsaron jihar Alabama ya bayyana, ba a da tabbacin me ya haifar da harbe-harben domin a nan take ba a san ko wanda ake zargi yana hannu ba.

Burkett ya bayyana cewa akwai mutane hudu da suka rasa ransu a wannan al'amari kuma da yawa sun samu raunuka.

CBS News ta ruwaito cewa harbe-harben sun girgiza dan karamin birnin mai dauke da mutane 3,200, tare da bayyana cewa an shirya kasancewa a farke a tsawon daren ranar Asabar domin gabatar da addu'o'i.

Mafi yawancin wadanda aka harbe din matasa ne, kuma dan uwan wadda ta ke bikin murnar ranar haihuwar shima an harbe shi kamar yadda wani mutum mai suna Ben Hayes ya fadawa Al.com a ranar Lahadi.

Shugaban jami'an 'yan sanda a Dadeville, Jonathan L. Floyed, ya bayyanawa Associated Press a yayin wani taro na 'yan jaridu cewa, "Abinda mu ke fama da shi ba kowacce al'umma ce za ta iya yin hakuri da shi ba. Ina rokon ku yi hakuri, zai kasance al'amari mai tsawo. Ina neman addu'o'in ku." 

An ruwaito cewa sama da awowi 12 bayan harbe-harben, jami'ai masu gudanar da bincike sun yi ta shiga tare da fita daga wurin mai suna Mahogany Masterpiece dance studio, kamar yadda wani allo ya nuna daga wajen wani ginin bulo mai hawa daya daga cikin garin na Dadeville. 

Manyan mutane a birnin da manyan jami'ai sun jeru a wani wuri da ake kira Tallapoosa County Courthouse, gini daya a tsakani, inda jami'ai suka sakko da tutocin Amurka da na Alabama kasa.

No comments

Powered by Blogger.