Mutane hudu sun rasa ransu yayin harbin da dan bindiga ya yi a birnin Louisville da ke Amurka
Akalla mutane hudu suka rasa rayukansu wasu takwas suka jikkata a yayin harbe-harben bindiga a Louisville da ke jihar Kentucky a Amurka, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.
Mataimakin shugaban 'yan sanda na yankin Louisville, Paul Humphrey, ya bayyanawa manema labaru cewa jami'an 'yan sanda da suka isa wurin da al'amarin ke faruwa "sun tarar da harbe-harben bindiga na cigaba da faruwa."
Jami'an 'yan sanda sun yi harbe-harben bindiga da wanda ke harbin, wanda tsohon ma'aikacin banki ne, amma ba a iya gane me ya haifar da rasuwar sa ba.
"Ba mu iya gane menene takamaimai dalilin rasa ransa ba." Kamar yadda Humphrey ya bayyana.
Shugaban 'yan sandan ya bayyana cewa 'yan sanda biyu na cikin mutane takwas da suke samun kulawar likitoci sakamakon harbin harsasai a asibiti.
Daya daga cikin 'yan sandan da kuma wani mutum daya suna cikin mawuyacin hali.
Hukumar FBI ta bayyana cewa ta kawo jami'an ta harabar da al'amarin ya faru.
Gwamnan jihar Kentucky, Andy Beshear, ya rubuta cewa zai tafi Louisville din, "Ina rokon ku, ku yi addu'a ga iyalan da wannan al'amari ya shafa kuma ku yi addu'a ga birnin Louisville."
Harbe-harben na ranar Litinin sune harbe-harbe na bayan nan a kasar Amurka, kuma suna zuwa ne sati biyu bayan an harbe mutane shida, cikinsu har da kananan yara, a wata makarantar kiristoci wadda ba ta gwamnati ba a Nashville da ke jihar Tennessee.
Post a Comment