Miliyoyin mutane sun fito domin gabatar da muzaharar ranar Quds a fadin duniya
Miliyoyin mutane sun fito a kasar Iran da sauran kasashen musulmai domin gabatar da muzaharar nuna boyon baya ga raunanan mutanen Falasdinu tare da yin Allah wadai da irin cin zarafin da Isra'ila ke yi.
A kasar Iran, kungiyar "Islamic Propagation Coordination Council (IPCC) ce ta shirya muzaharar, kuma an fara ta ne da misalin karfe 10:00 na safe a birnin Tehran da sauran biranen kasar a ranar Juma'a.
A kowacce Juma'ar karshen watan Ramadan, ana gabatar da muzaharori domin nuna goyon baya ga fafutikar Falasdinawa kan Isra'ila kan kokarin da suke yi na kwatar kasar su wadda aka mamaye tun shekarar 1967.
Al'amarin ana ganinsa a matsayin wata dama ga masu neman 'yanci a fadin duniya, ba tare da la'akari da imanin su ba, su yi magana kan goyon bayansu ga fafutikar Falasdinawa da kuma nuna fushinsu kan Isra'ila.
Ayatollah Imam Khomeini, wanda ya ke babban jagora ne a duniyar musulunci, shi ya sa ma Juma'ar karshe ta kowanne watan Ramadan sunan ranar Quds a shekarar 1979, jim kadan bayan ya jagoranci tabbatar da kasancewar Jamhuriyar Musulunci tare da hambarar da mulkin da Amurka ke goyon baya na Shah a kasar Iran.
Kakakin majalisar kasar Iran, Mohammad Baqer Qalibaf , ya bayyana cewa yin fafutika ce hanya daya ta samun nasara a kan kasar Isra'ila.
"Ranar Quds rana ce mai matukar muhimmanci ga al'ummar musulmai da kasashen musulmai. Ranar Quds na nuni ne da cewa ana samun nasara ne kawai ta hanyar fafutika." Kamar yadda ya fadawa masu muzahara a Tehran.
"Al'amarin da ya shafi Falasdinawa rayayye ne. Ko a wasanni kamar Kwallon Duniya na FIFA (a Qatar) mun ga goyon baya ga Falasdinawa da fafutikar Falasdinawa. Wannan goyon bayan ba na musulmai ba ne kawai, har ma da na wadanda ke neman 'yan ci a fadin duniya." Kamar yadda ya bayyana.
Post a Comment