Header Ads

Me ya sa aka tsare Peter Obi a Landan?

Mista Peter Obi na Labor Party

Jami'an shigi-da-fici na kasar Ingila sun tsare dan takarar shugaban kasa a Nijeriya a karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi, a ranar Good Friday a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Heathrow da ke Landan sakamakon akwai wani da ke kwaikwayonsa. 

Diran Onifade, shugaban kungiyar watsa labaru ta Obi-Datti, a cikin wani jawabi a ranar Laraba, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasar ya isa filin jiragen sama na kasa-da-kasa na Heathrow da ke Landan a ranar Good Friday, 7 ga watan Afirilun shekarar 2023, ya kuma bi layi domin cika duk wasu ka'idoji na filin jirgin sama, kawai sai jami'an shigi-da-fici suka kawo masa takardar tsarewa tare da umartar sa da ya koma gefe.

Onifade ya bayyana cewa an yi wa Obi tambayoyi na lokaci mai tsawo, kuma abin mamaki ne a ce an yi wa wani mutum da ya zauna a wannan kasa na lokaci mai tsawo haka.

Ya bayyana cewa an ruga an san fuskar Obi a cikin kasashen duniya, musamman ga 'yan Nijeriya, 'yan Afirka da kuma wadanda suke zaune a wasu kasashen musamman magoya bayansa (Obedients), mutanen nan da nan suka yi magana suna mamakin me zai sa a bata masa lokaci.

Onifade ya bayyana cewa jami'an shigi-da-ficin wadanda suka cika da mamakin yadda mutane suka dauki abin dole ta sa suka bayyana cewa ana yi wa Obi tambayoyi ne saboda kasancewar bayanansa biyu ne, wato akwai wanda ke kwaikwayonsa a Landan.

Ya bayyana cewa babbar matsalar hakan shine wanda ya ke kwaikwayonsa din zai iya ya dunga yin manyan laifuka da sauran abubuwan da ba su dace ba kuma za a dauke su ne a matsayin sunan Obi.

No comments

Powered by Blogger.