Header Ads

Makaman roka daga Siriya sun sauka a yankin Golan Heights da Isra'ila ta mamaye

Wasu makaman roka da aka harba

Sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa an harbo makaman roka uku daga bangaren kasar Syria zuwa yankin da Isra'ila ta mamaye na Golan Heights.

Al'amarin ya faru ne a ranar Asabar, inda sojojin Isra'ilan suka yi ikirarin cewa "daya daga cikin rokokin" ya tsallaka zuwa yankin da Isra'ila ke iko da shi "tare da fadawa wani wurin da ba komai" a kudancin yankin Golan Heights.

Ba wani rahoton da ya gaggawa bayyana cewa an samu rauni ko asarar dukiya.

Harin rokokin na zuwa ne a yayin da ake cikin zaman dar-dar a yankunan da aka mamaye din da sauran wurare sakamakon hare-hare akai-akai da Isra'ilan ke kaiwa masu gabatar da ibada Falasdinawa a harabar masallacin al-Aqsa - wanda shine wuri mafi tsarki na uku a musulunci - tun ranar Laraba. 

A hari na farko, jami'an tsaron Isra'ilan sun afka harabar masallacin na al-Aqsa inda suka runka dukan masu gabatar da ibada, daga bisani kuma suka kama su suka kuma tursasa fitowa da su kusan su 100. Falasdinawa da dama an raunata su a sakamakon wannan hatsaniya.

Lokaci kadan bayan faruwar wannan al'amari sai aka harbo rokoki daga yankin Falasdinawa na Gaza domin daukar fansa. Kwana daya bayan nan, aka harbo wasu rokokin daga kasar Lebanon.

Isara'ila kuma sai ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare ta jiragen sama a cikin Gaza din da kasar Lebanon a ranar Juma'a.

A yayin da suke bayani game da al'amarin wanda suka yi ikirarin faruwarsa a ranar Asabar, sojojin na Isra'ila sun ce da fari an fara jin karar gargadin makamin roka a yankin.

Sojojin Isra'ila sun kwace yankin Golan Heights ne daga kasar Syria a yayin yakin kwanaki 6 da aka yi a cikin shekarar 1967, sai kuma daga baya ta mamaye shi, wani al'amari wanda mafi yawancin kasashen duniya ba su amince da shi ba.

No comments

Powered by Blogger.