Header Ads

Majalisar kasashen Larabawa ta yi taron gaggawa tare da yin Allah wadai da harin Isra'ila a kan masallacin al-Aqsa

Wasu 'yan sandan Isra'ila sun kama wani mutum Bafalasdine a harabar masallacin al-Aqsa da ke gabashin Jerusalem a Falasdin, a ranar 5 ga watan Afirilun shekarar 2023.

Majalisar kasashen larabawa ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai masallacin al-Aqsa da ke birnin al-Quds da aka mamaye tare kuma da harin da ta kai kan Falasdinawa masu gabatar da ibada a cikin wata mai alfarma na Ramadan.

Majalisar mai mambobin kasashe 22 ta yi taron gaggawa domin tattaunawa dangane da kutsawa wannan muhalli mai tsarki na musulmai tare kuma da afkawa musulmai masu gabatar da ibada a wurin.

"Da kakkausar murya, muna yin Allah wadai da laifuffukan da gwamnatin mamaya ke aikatawa a kan masu ibada marasa makami a masallacin al-Aqsa." Kwamitin ministoci na majalisar kasashen larabawan ya bayyana a cikin wani jawabi.

"Da kakkausar murya muna yin Allah wadai da duk wata keta alfarma ko hari na kasar mamayar a kan wurare masu tsarki na musulunci ko kiristanci."

Majalisar ta tabbatar da hakkin da musulmai da kiristoci ke da shi na zuwa wuraren ibadar su ba tare da takurawa ba kuma su yi wa'azi ba tare da takurawa ba tare da yin ayyukan da suka shafi imanin su.

Majalisar ta bayyana cewa matakan na Isra'ila laifuffuka ne da ke hana 'yancin gudanar da ibada ga musulmai da kiristoci a wurare masu tsarki da aka mamaye na al-Quds, inda majalisar ta larabawa ta kara da cewa wadannan matakai karya dokokin majalisar dinkin duniya ne, dokar kasa-da-kasa da kuma dokar agajin gaggawa ta kasa-da-kasa. 

"Wadannan harbe-haren da laifuffukan tonan fada ne ga wadanda suka yi imani na ko'ina, kuma neman tayar da fada ne wanda zai yi barazana ga tsaro da daidaituwar yankin da kuma duniya." Kamar yadda majalisar ta yi gargadi.

Kwamitin ya yi kira ga mambobin kasashen da su yi duk wani abinda ya dace a kowanne mataki, domin samar da kariya ga birnin al-Quds, kare wurare masu tsarkin sa na musulunci da kirsitanci da kuma nuna goyon baya ga siyasa, yanayin zamantakewar al'umma, tattalin arzuki da kuma hakkin bil-adama na mutanensa. 

Jami'an tsaron Isra'ila masu yawa ne dai suka kutsa harabar masallacin al-Aqsa a daren ranar Talata daga bisani kuma suka fara harba barkonun tsohuwa (tear gas) da gurneti a cikin ginin da ake yin sallah, inda daruruwan maza, mata, tsofaffi da yara ke tsayawa tsawon dare suna sallah. Wasu shaidun gani da ido ma sun bayyana cewa har harsasai an harba.

Sai kuma 'yan sandan na Isra'ila suka fara dukan masu gabatar da ibada da sanduna da kuma bindigogin kwantar da tarzoma, inda suka raunata da dama kafin su kama su.

Bidiyoyi daga cikin ginin sun nuna jami'an tsaron na dukan masu gabatar da ibadar da bindigogi a yayin da su kuma a dukkan alamu suke a kwance a kasa. Kuma ana jin kukan neman taimako daga mata da yara a bidiyon.

Tun shigowar wannan wata mai alfarma, gwamnatin Isra'ila ta mayar da shigowa da fitar Falasdinawa ta kofofin al-Aqsa da wahala sosai. A yayin da zaman dar-dar ya karu sosai, Yahudawa 'yan kama wuri zauna sun cigaba da kutsowa suna yin wasu ayyuka nasu na tonon fada a wuraren masu tsarki.

No comments

Powered by Blogger.