Header Ads

Kungiyar Islamic Jihad ta yi Allah wadai da kutsawar sojojin Isra'ila cikin masallacin al-Aqsa

Sojojin Isra'ila yayin da suka kutsa harabar da ake yin sallah na Bab al-Rahman ta hanyar katangar gabas a harabar masallacin al-Aqsa wanda ke a tsohon birnin al-Quds a ranar 22 ga watan Afirilun shekarar 2023

Kungiyar fafutikar Falasdinawa ta Islamic Jihad ta yi Allah wadai da kutsawar sojojin Isra'ila cikin wurin da ake gudanar da sallah ta bangaren katangar gabas na harabar masallacin al-Aqsa, inda ta tabbatar da aniyar ta na kare tsarkin wurin duk da yadda Tel Aviv ke keta alfarmarsa .

Mai magana da yawun kungiyar fafutika ta Islamic Jihad, Tariq Salmi, a cikin wani jawabi, ya nuna rashin dacewar kutsawa harabar da ake gabatar da sallah ta Bab al-Rahman (Kofar Rahama) da aka yi, inda ya bayyana cewa, "Wannan matakin na cikin yunkurin gwamnatin mamaya na keta alfarmar wurare masu tsarki."

"Mutanenmu za su cigaba da kare kasarsu da wurarensu masu tsarki kuma ba za su taba barin aikin su ga masallaci mai alfarma na al-Aqsa ba." Salmi ya tabbatar.

Kakakin ya bayyana cewa Bab al-Rahman harabar masallacin al-Aqsa ne, kuma yunkurin gwamnatin mamaya na yin iko da shi ba zai yi nasara ba, inda ya bayyana cewa duk wani yunkuri na yin abinda bai kamata ba ga masallacin al-Aqsa ko kuma wasu wurare nasa masu tsarki zai haifar da babban martani daga mayakan masu fafutika da kuma martani daga yankunan gabas ta tsakiya. 

Kamar yadda kafar watsa labarun Falasdinawa ta Wafa ta bayyana, a ranar Asabar ne dai sojojin na Isra'ila suka kutsa harabar da ake yin sallah ta Bab al-Rahman, inda suka lalata wutar lantarki da lasifikoki da ke ciki a yayin da mutane ke gudanar da bikin Idi wanda ke nuni da kawo karshen azumin watan Ramadan.

Kimanin Falasdinawa 120,000 ne suka yi sallar Idi a harabar masallacin na al-Aqsa a ranar Juma'a duk da tsauraran matakan da Isra'ila ta dauka.

No comments

Powered by Blogger.