Kasar Koriya ta Arewa ta harba wani sabon samfarin makami mai linzami
Kasar Koriya ta Arewa ta harba wani sabon samfarin makami mai linzami a ranar Alhamis kamar yadda kasar Koriya ta Kudu ta bayyana.
Mazauna a yankunan arewacin kasar Japan wadanda suka tsorata da al'amarin an bukace su da su kasance cikin shiri, duk da cewa ba wani hatsari a fili.
Wani jami'in soja a kasar Koriya ta Kudu ya bayyana cewa makami mai linzamin wani samfarin makami ne wanda aka yi amfani da shi a yayin faretin sojoji na baya-bayan nan kuma ya na amfani da "Solid Fuel" ne.
Sojojin kasar Koriya ta Kudu sun bayyana cewa makamin ya tashi tsawon kilomita 1000 (mil 620), inda suka bayyana na shi da "babban tonon fada."
Kamar yadda jami'ai suka bayyana, nisan makamin na karshe bai kai kilomita 6,000 ba, wanda shi ne karshen nisan makaman da a ka gwada na bayan nan a shekarar da ta gabata.
"A yanzu mun tabbatar da cewa sun harba sabon makami wanda ke da matsakaicin nisa ko kuma na iya zuwa kowacce nahiya." Jami'in ya bayyana, "A yanzu haka muna duba abubuwa kamar hanyoyin da zai iya bi, tsawon da zai kai a sararin samaniya da nisan da zai iya kaiwa, kuma akwai yiwuwar man da ake sa masa " Solid Fuel" ne."
Sojojin Koriya ta Kudu sun ce suna a shirye kuma suna tare da babbar kawarsu Amurka wadda da "Kakkausar murya ta yi Allah wadai" da abinda ta kira gwada makami mai cin dogon zango.
An dai harba makami mai linzamin ne da karfe 7:23 na safe a kusa da Pyongyang, kamar yadda sojojin Koriya ta Kudu suka bayyana, inda su kuma masu tsaron gabar ruwan kasar Japan suka bayyana cewa ya sauka da karfe 8:19 na safe.
Post a Comment