Jami'an tsaron sun sake bude wuta kan masu muzaharar a ba Sheikh Zakzaky fasfonsa
Hayakin barkonun tsohuwa ya tashi sama yayin da rundunar jami'an tsaron Nijeriya ke harbo su ga masu muzahara
A ranar Alhamis, 30 ga watan Macin shekarar 2023, jami'an tsaron Nijeriya suka sake yin amfani da harsasai masu rai akan almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky, a wannan karon a kan wadanda ke kira ga gwamnatin da ta bayar da fasfo dinsa da na mai dakinsa domin su fita neman lafiya a garin Abuja, lokaci kadan bayan alkalin kotun Federal High Court din da ke Abuja, Alkali Obiora Atuegwu Egwuatu, ya yanke hukuncin cewa ba zai bada oda a sake yiwa shehin malamin fasfo ba dalili kuwa saboda a cewar sa wadanda suka kawo kara ba su kawo hujjoji wadanda ya dace su kawo a shari'a domin ya ba da odar a yi sabon fasfo ba.
Bayan yanke hukuncin kotun ne da kuma jawabin da daya daga cikin lauyoyinsa shehin malamin, Barista Haruna Magashi, ya yi ga manema labaru, sai almajiran shehin malaman da ke harabar kotun suka hau kan titi domin gudanar da muzahara kamar yadda kafar Ahlulbayt Broadcasting Services (ABS) a kafar sada zumunta ta Facebook ta bayyana a wani bidiyo.
Kamar yadda kafar ta ABS ta bayyana a bidiyon, bayan jawabin lauyan shehin malamin, sai matasan da ke bakin kotun suka hau sahu tare da gudanar da muzahara, ana kira ga gwamnati da ta gaggauta ba Sheikh Zakzaky fasfo dinsa tare da na mai dakinsa da kin yarda da rashin adalcin da kotu ta yi.
An dai runka rera wakoki da baitocin "We are ready to die for Zakzaky", "Allahu Akbar" da sauransu yayin muzaharar, kuma ta taso ne daga bakin kotun inda ta ratsa ta iso har Federal Secretariat, kuma tana tafiya cikin lafiya, daga bisani aka yi kwana aka sake haurowa da muzahara, sai dai ana zuwa junction din Eagle Square sai ga rundunar jami'an tsaron Nijeriya, inda suka afkawa masu muzaharar da harbin barkonun tsohuwa (tear gas) biyo bayan tear gas din, sai masu muzaharar suka tunkare su da kabbara, kawai kuma sai jami'an tsaron suka fara amfani da harsasai masu rai a kan masu muzaharar inda suka yi ta harbin bindiga babu kakkautawa.
Kamar yadda ya ke a bidiyon, zuwa lokacin yin rahoton ba a samu rahoton wani ya yi shahada ba, amma dai an harbi masu muzaharar masu yawa.
Post a Comment