Jami'an tsaro sun harbe matashi tare da jikkata wasu 20 yayin muzaharar Qudus ta bana
Muzaharar Quds muzahara ce wadda aka saba gabatarwa a kowacce Juma'ar karshen watan Ramadan a fadin duniya domin nuna goyon baya ga fafutikar Falasdinawa kan Isra'ila a kan kokarin da suke yi na kwatar kasar su wadda aka mamaye tun shekarar 1967.
A wannan shekarar, muzaharar Quds an gabatar da ita a fadin duniya a ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2023, ciki kuwa har da kasar Nijeriya, sai dai a yayin da a wurare da dama a duniya an kammala ta lafiya, a Nijeriya, jami'an tsaro sun harbe yaro daya tare da jikkata wasu mutum 20.
A Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, jami'an 'yan sanda sun bude wuta da harsasai masu rai a kan masu gudanar da muzaharar Quds wadda ta ke ta zaman lafiya, inda suka harbe wani yaro dan shekara 15 tare da jikkata da dama.
Maryam Gashua, shugabar Shuhada Foundation ta Harkar Musulunci a Nijeriya ta tabbatar da harin ga wani wakilin Iran Press ta hanyar wayar tarho.
Wani shaidan gani da ido, Isa Charis, ya bayyana cewa muzaharar wadda ta taso daga masallacin Fu'ad ta taso lafiya kalau har sai lokacin da jami'an 'yan sanda suka zo suka fara harbin mutane wanda hakan ne ya yi sanadiyyar shahadar yaro dan shekara 15, Yaqoub Umar, wanda aka fi sani da Khalifa nan take tare da jikkata da dama.
A jihar Kaduna ma, akalla mutane 20 ne suka jikkata a lokacin da jami'an 'yan sandan suka bude wuta ga masu gudanar da muzaharar ta Quds.
A ranar 25 ga watan Yulin shekarar 2014, akalla mutane 35 wadanda ba dauke da makami suke ba jami'an tsaro a Nijeriya na hadin gwiwa suka harbe a ranar Quds, a cikin wadanda suka yi shahada a wannan lokaci akwai Ahmad Ibrahim Zakzaky, Hamid Ibrahim Zakzaky da Mahmud Ibrahim Zakzaky, wadanda dukkan su 'ya 'ya ne ga shugaban Harkar Musulunci a Nijeriya.
A cikin wata tattaunawa da ya yi da Iran Press a cikin satin da ya gabata, wani jigo a Harkar Musulunci a Nijeriya, Farfesa Abdullahi Danladi, ya zargi gwamnatin Nijeriya da kasancewa 'yar amshin shatan kasashen yamma.
"Gwamnatin Nijeriya na yiwa kasashen yamma aiki ne, kasashen yamma kuwa Isra'ila ce ke iko da su. Saboda haka in mun fito muna nuna goyon bayanmu ga Falasdinawa, gwamnatin Nijeriya ba ta jin dadin hakan domin haka din yin fito-na-fito ne da shugabannin su." Kamar yadda Farfesan ya bayyana.
A wannan karon dai an gudanar da muzahar ta Quds a garuruwan da dama a Nijeriya wadanda suka hada babban birnin tarayya Abuja, Kaduna, Bauchi, Sokoto, Nguru, Mashi, Azare, Potiskum, Lafia, Katsina, Zaria, Gombe, Yola, Jibia, Gashuwa, Kano, Jos, Birnin Kebbi, Dutsinma, Talatar Mafara, Dandume, Zuru, Ilela, Legas.
Post a Comment