Header Ads

Isra'ila ta kara harba makamai masu linzami zuwa Siriya

Wani makami mai linzami mallakin Isra'ila

Kasar Isra'ila ta kara kai sabbin hare-hare da makamai masu linzami a babban birnin kasar Siriya, Damascus, a yayin da kasar masu mamayar ke cigaba da ayyukanta da ke cutarwa ga kasar ta larabawa.

Tashar watsa labaru ta kasar ta Siriya, SANA news agency, ta ruwaito wata majiyar sojoji na fadin cewa an harbo makamai masu linzami da dama na Isra'ila daga yankin Golan Heights wanda aka mamaye zuwa wuraren da ke kusa da Damascus, inda aka ji karar fashewa a birnin kasar.

Majiyar ta bayyana cewa makaman tsaron sararin samaniyar Siriya sun tarbi makaman masu linzamin na Isra'ila inda suka kabe da dama, kuma makaman masu linzamin sun haifar da asarar dukiya inda kuma wasu sojoji biyu suka raunata.

Daga baya Ma'aikatar Tsaron Siriya ta tabbatar da harin, amma ba ta yi bayani dangane da inda aka yi nufin hara ba.

"Da misalin karfe 01:20 na dare, abokan gaba Isra'ila suka kawo hare-hare ta sama daga yankin Golan Heights wanda aka mamaye zuwa wasu wurare da ke harabar Damascus." Kamar yadda suka bayyana.

Wannan harin na zuwa ne sati daya bayan Isra'ilan ta kai hari a filin saukar jiragen sama na kasa-da-kasa da ke arewa-maso-yammacin birnin Aleppo, inda ya haifar da "asarar dukiyoyi" sannan kuma ayyukan filin jirgin saman suka tsaya tsak.

Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen kasar Siriya ta yi Allah wadai da harin, inda ta bayyana shi da "laifi biyu" domin kuwa an yi shi ne a filin jiragen sama na fararen hula kuma a kan hanyar wucewa da kayan jin kai ga wadanda ibtila'in girgizar kasa ya shafa a kasar a cikin watan Fabrairu. 

Harin shine na uku a filin jirgin sama na Aleppo a cikin watanni shida. 

Isra'ila kan yi shiri a kan hare-haren da ta ke kai wa cikin kasar Siriya, kuma kasar ta Siriya ta sha kai koken ta ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya domin a dauki mataki a kan Tel Aviv, sai dai ba a sauraron koken.

No comments

Powered by Blogger.