Header Ads

Iska mai karfin gaske ta kashe da dama da lalata dukiyoyi a Amurka

Wani wuri da iskar ta yi barna

Ibtila'in iska mai karfin gaske da ta bi ta tsakiyar Amurka da kuma yankin kudancin kasar ta yi sanadiyyar rasuwar akalla mutane hudu a yayin da dama suka jikkata.

A yankin kudancin jihar Arkansas da garuruwan da ke kusa da ita, guguwa mai karfin gaske ta yi sanadiyyar rasuwar akalla mutane uku, ta rushe katangun gine-gine da dama, ta hambarar da motoci, ta karya bishiyoyi tare da karya layukan wutar lantarki.

"Wannan ba karamar guguwa ba ce mai lalata abubuwa." Wani wanda ya ke ganau ne ga al'amarin mai suna Lara Farra ya shaidawa AFP, "Gabadaya ina cikin rudani domin baki daya wannan yanki ya rushe duka." Kamar yadda ya bayyana.

"Abubuwa da yawa sun rushe a tsakiyar Arkansas." Gwamnar jihar Arkansas, Sarah Huckabee Sanders, ta rubuta a shafin ta na Twitter.

Kamar yadda Poweroutage.us ta bayyana, sama da mutane 78,000 suka rasa wutar lantarki a jihar.

Iska mai karfi daban-daban ta bi ta tsakiyar kasar da kuma Illinois, inda mutum daya ya mutu yayin da miliyoyin mutane suke karkashin kulawa daga guguwa mai karfi a jihohin Texas zuwa Wisconsin, Iowa zuwa Mississippi zuwa Michigan.

Wannan ibtila'in na zuwa ne sati daya bayan ruwan sama mai karfi wanda zai iya kasancewa da tsawa akai-akai ya haifar da guguwa mai karfin gaske wadda ta yi kaca-kaca da garin Rolling Fork da ke jihar Mississippi, inda kuma wasu gidaje 400 suka rushe mutane 26 kuma suka rasa rayukansu. 

A kasar Amurka, ibtila'in guguwa mai karfi wani abu ne da aka saba ganinsa, musamman a tsakiya da kuma kudancin kasar.

No comments

Powered by Blogger.