Header Ads

Iran za ta fara sufurin jiragen sama akai-akai zuwa Saudiyya a kowane mako

Wani jirgin saman kamfanin Iran

Kasar Iran na shirye-shiryen fara yin sufurin jiragen sama akai-akai zuwa kasar Saudi Arabiya sakamakon neman ta yi hakan da Riyadh ta yi a yayin da ake kara samun jituwar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Ministan Sufuri na kasar Iran, Mehrdad Bazrpash, a ranar Lahadi ya bayyana cewa hukumomin Saudi Arabiya sun nemi kasar Iran da ta fara yin sufurin jiragen sama sau uku a sati zuwa kasar ta Larabawa.

Bazrpash ya bayyana cewa sufurin jiragen saman za a fara ta ne ba tare da la'akari da shirye-shiryen da ke tsakanin kasashen biyu dangane da jigilar alhazan Iran zuwa hajji a Saudiyya ba.

"An fara tunanin gudanar da sufurin jiragen sama a tsakanin Saudiyya da Iran bayan jigilar alhazai domin kara fadada dangantaka." Kamar yadda ministan ya bayyana, inda ya kara da cewa Iran za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin fara yin sufurin.

Wannan sanarwa na zuwa ne a yayin da kasashen na Iran da Saudi Arabiya ke shirye-shiryen bude ofisoshin jakadancinsu domin dawo da huldar diflomasiyya bayan sun yanke huldar shekaru bakwai da suka gabata a hukumance.

Shirin na cikin wata yarjejeniya ce wadda kasar Sin ta jagoranta a farkon watan Maci wadda ta tanaji cewa kasashen musulman biyu su dawo da huldar su ta diflomasiyya zuwa 9 ga watan Mayu. 

Masana sun bayyana cewa dawo da wannan dangantaka za ta samar da habakar alaka ta tattalin arzuki da sufuri a tsakanin kasashen biyu.

No comments

Powered by Blogger.