Header Ads

Iran ta yi barazanar harbo wani jirgin leken asiri na Amurka bayan ya yi kusa da ya kutsa sararin samaniyar ta - Rundunar sojojin ruwan Amurka

Jirgin sojojin ruwa na Amurka EP-3E

A ranar Asabar, 2 ga watan Afirilun shekarar 2023, kafofin watsa labarun Iran suka ruwaito cewa rundunar sojojin ruwa ta kasar ta gargadi wani jirgin leken asiri na Amurka da ya gujewa shigowa sararin samaniyar ta a bangaren tekun Oman. 

Kafar watsa labaru ta Tasnim, ta yi ikirarin cewa jirgin saman na EP-3E mallakin rundunar sojojin ruwan Amurka yana gaf da kutsawa cikin sararin samaniyar Iran ne ta bangaren tekun Oman sai rundunar sojojin ruwan Iran suka katse hakan tare da yin gargadi ga jirgin mai shirin yin kutse.

Kafar watsa labarun ba ta bayar da cikakken bayani ba a bayan haka, amma ta bayyana cewa jirgin na Amurka ya fasa tare da komawa sararin samaniyar kowa-da-kowa na kasa-da-kasa.

Ofishin Amurka da ke kula da duk wasu harkoki na soja a gabas ta tsakiya bai yi magana a kan al'amarin ba.

Kasar Iran da Amurka a baya sun taba samun arangama sakamakon jirgin Amurka da ya shiga sararin samaniyar kasar Iran. Misali, a cikin shekarar 2019, Iran ta harbo jirgin sama mara matuki na sojojin ruwan Amurka HQ-4A Global Hawk High-Altitude, Long, Endurance (Hale) ta hanyar amfani da mizayel wanda ake harbawa daga sarari zuwa sama a mashigar ruwa ta Hormuz.

A cikin watan Disambar 2011, Iran ta yi ikirarin cewa ta harbo jirgin saman Amurka RQ-170 Sentinel wanda ta ce ya shiga sararin samaniyar ta.

A baya-bayan nan kuma, zaman dar-dar ya kara lunkuwa tsakanin Amurka da Iran. Wasu kasashen na maganganu cewa Iran ta taimakawa kasar Rasha da jirage marasa matuki a yayin da ta ke yaki da Ukraine.

Amurka ta sanyawa kamfanonin kera jirage marasa matuka na Iran din takunkumi, sai dai Iran ta bayyana cewa ta aika da jirage marasa matuka Rasha, to amma kafin a fara yakin Ukraine ne a shekarar 2022.

No comments

Powered by Blogger.