Ingila ta sa likitocin Nijeriya da na wasu kasashe 53 cikin jerin wadanda ba za ta ci gaba da dauka aiki ba
Ingila ta sa Nijeriya da wasu kasashe 53 cikin kasashen da bangaren lafiyar ta da kulawa da jama'a ba za su runka daukar ma'aikatan lafiya ba.
Wannan na zuwa ne wata daya bayan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sa Nijeriya da wasu kasashe 55 cikin jerin kasashen da ke bukatar ma'aikatan lafiya in an yi la'akari da yadda ake bukata kamar a sauran sassan duniya.
Bayan Indiya da Pakistan, Nijeriya ce kasa ta uku da ta fi yawan likitoci da ke aiki a kasar Ingila.
A cikin wani gyara da ta yi a tsarin ayyukanta, Ingila ta bayyana cewa bangaren lafiya da kula da jama'ar ta ba ya daukar ma'aikata daga kasashen da WHO ta bayyana cewa suna da bukatar ma'aikatan lafiya, saidai in akwai yarjejeniya a tsakanin gwamnati da gwamnati domin yin taimako ga tsare-tsaren daukar aikin.
Ana bukatar masu daukar aiki, hukumomi masu daukar ma'aikata, hadin gwiwa da kungiyoyi masu kwantaragi su duba jerin kasashen kafin su dauki aiki.
Kasashen da aka sa a jerin "wadanda ba za a dauki aiki daga garesu ba" sun hada da Afghanistan, Angola, Bangladesh, Benin, Burkina Faso, Burundi, Cameroon, Central African Republic, Chad, Comoros, Congo, Democratic Republic of Congo, Cote d'Ivoire, Djibouti, Equatorial Guinea, Eritrea, Ethiopia, Gabon, The Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Haiti, Kiribati, Lao People's Democratic Republic, Lesotho, Liberia.
Sauran kasashen sun hada da Madagascar, Malawi, Mali, Mauritania, Federated States of Micronesia, Mozambique, Niger, Nigeria, Pakistan, Papua New Guinea, Rwanda, Samoa, Senegal, Sierra Leon, Solomon Islands, Somalia, South Sudan, Sudan, United Republic of Tanzania, Timor-leste, Togo, Tuvalu, Uganda, Vanuatu, Republic of Yemen, Zambia da kuma Zimbabwe.
Post a Comment