Header Ads

Hukumar aikin Hajji ta kasa ta bayyana kudin aikin Hajjin shekarar 2023

Hukumar aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta bayyana kudin aikin hajjin bana, wato shekarar 2023.

Hukumar ta sa kudin kujerar aikin hajji ga duk wani maniyyaci a Nijeriya kusa da naira miliyan uku.

A yayin da ya ke bayyana kudin aikin hajjin a cibiyar ta NAHCON da ke Abuja, shugaban hukumar aikin hajjin a Nijeriya, Zikirullah Kunle Hassan, ya bayyana cewa mahajjata da za su tashi daga Yola da Maiduguri za su biya naira 2,800,000 a yayin da wadanda kuma za su tashi daga sauran jihohin arewacin Nijeriya za su biya naira 2,919,000.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa kudancin kasar nan na da farashin kujerar aikin hajjin daban-daban har guda shida, inda ya bayyana cewa mahajjata daga jihar Edo za su biya naira 2,968,000 a yayin da kuma wadanda suka fito daga Ekiti da Ondo za su biya naira 2,180,000.

Mahajjata masu zuwa aikin hajji daga jihar Cross River za su biya naira 2,943,000, wadanda suka fito daga jihar Osun za su biya naira 2,983,000, mahajjata daga Legas, Ogun da Oyo kuma za su biya naira 2,999,000.

Mista Hassan ya bayyana cewa mahajjata daga jihohin kudu-maso-kudu da kudu-maso-gabashin kasar nan za su biya 2,968,000.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa banbance-banbancen kudaden aikin hajjin ya faru ne sakamakon banbanci na kudin tafiye-tafiyen domin wasu wuraren suna kusa da Saudi Arabiya fiye da wasu wuraren. 

Ya ma bayyana cewa bayan tattaunawa a tsakaninsu da shugabannin sashen zartarwa na hukumomin aikin hajji na jihohi, sun amince cewa shafin wadanda ke biya ta Hajj Saving Scheme za a kulle shi a ranar (wato Juma'a 7 ga watan Afirilun shekarar 2023).

Ya ma kara da cewa a yayin tattaunawar an amince cewa duka wasu maniyyata aikin hajjin su kammala biyan kudadensu kafin ranar 21 ga watan Afirilun 2023.

No comments

Powered by Blogger.