Header Ads

Hatsarin yin arangama da makaman nukiliya kai tsaye da Amurka na kara hauhawa - Rasha


Kasar Rasha ta yi gargadin cewa hatsarin yin arangama kai tsaye da makaman nukiliya da kasar Amurka na kara hauhawa sakamakon irin dabi'un da Amurka din ke nunawa tun fara yakin kasar Ukraine.

Daraktan hana yaduwar makaman nukiliya da kayyade makamai na sashen Ma'aikatar Kasashen Wajen kasar Rasha, Vladimir Yermakov, ne ya yi gargadin a cikin wata tattaunawa da ya yi da kafar watsa labarun kasar Rasha, TASS, a ranar Talata.

"In har Amurka ta cigaba da bin wannan hanyar da ta ke bi ta yin fito-na-fito da Rasha tare da kara yiwuwar yin arangamar soja kai tsaye, to fatar da ake da ita ta yarjejeniyar New START za ta zo karshe."

An dai yi yarjejeniyar New START ne a cikin watan Afirilun shekarar 2010 a tsakanin tsohon shugaban kasar Amurka, Barrack Obama, da takwaransa na Rasha, Dmitry Medvedev, inda suka amince da rage yawan makaman nukiliya zuwa rabi tare da rage yawan makaman nukiliya da aka girke zuwa 1,550, inda wannan adadi shine mafi karanci a cikin shekaru da dama.

An kara tsawon yarjejeniyar ta New START a cikin watan Fabrairun shekarar 2021 zuwa watan Fabrairu na shekarar 2026, wanda shugaban kasar Amurka, Joe Biden da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, suka yi.

To sai dai a ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2023, Rasha ta dage kasancewar ta cikin yarjejeniyar a yayin da Washington ke kara aiwatar da tsare-tsare da ke yin fito-na-fito da Moscow. Ba ta janye baki daya daga yarjejeniyar ba, inda ta fayyace cewa za ta cigaba da bin ka'idar yawan makaman da aka girke a cikin yarjejeniyar ta New START.

"...A yanayi mafi ban tsoro, in har Amurka ta cigaba da jan wannan yanayin har ya kai ga arangamar soja a tsakanin kasashen da suka fi kowacce karfin makamin nukiliya, to ba fatar New START ba ne abin tunani, amma fatar duka duniya ce abin tunani." Yermakov ya bayyana.

"Wannan ya kara tabbatar da cewa babbar barazana ba tana tare da fara kai babban hari bane, wanda yarjejeniyar New START ke kokarin hana afkuwarsa, hatsarin na tare da yiwuwar amfani da makaman nukiliya sakamakon arangamar soja a tsakanin kasashe masu karfin makamin nukiliya." Yermakov ya bayyana, inda ya kara da cewa, "Kuma muna da na sanin cewa wannan hatsarin na kara hauhawa."

Dan diflomasiyyar ya bayyana cewa domin a rage wannan zaman dar-dar dole Amurka ta dauki matakan hana ta'azzarar abubuwa tare da yin watsi da matsayar da ta dauka na yin cikas ga tsaron Rasha a aikace.

Yermakov na magana ne dangane da cigaba da taimakon soji da Amurka ke yi ga kasar Ukraine wadda ke yaki da Rasha.

Washington dai ta bayyana cewa ta kai taimakon soji har sau 36 ga Kiev tun fara yaki a watan Fabrairu da ya gabata, inda hakan ya nuna cewa taimakon Amurka ga Ukraine ya kai sama da dalar Amurka biliyan 35. 

Dan diflomasiyyar na kuma yin nuni ne ga taimakon da Washington ke yi na kara fadada hadakar NATO da Amurka ke jagoranta a kan iyakar Rasha.

No comments

Powered by Blogger.