Harkar Musulunci a Nijeriya ta shigar da kara a kotun duniya kan kisan kiyashi ga 'yan Shi'a a jihar Kaduna
Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN) ta nemi kotun hukunta laifuffuka ta duniya (ICC) da ta yi bincike tare da yanke hukunci ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, kan ikirarin aiwatar da kisan kiyashi a kan 'yan Shi'a a jihar Kaduna.
A yayin da ya ke magana a Abuja a ranar Asabar, 15 ga watan Afirilun 2023, Lauyan na IMN, Lawal Dakum, ya yi ikirarin cewa tun fara mulkin El-Rufai a cikin shekarar 2015, ya yi ta aiwatar da laifuffuka da abubuwa na kisan kiyashi a kan 'yan Shi'ar wanda niyyar hakan shine karar da 'yan Shi'ar a jihar Kaduna.
"Wadanda muke karewa sun ga bala'o'i da hare-hare wadanda ba tono su suka yi ba tun bayan tsararren kisan kiyashin Zaria, inda musulmai sama da 1,000 'yan Shi'a aka kashe.
"Mafi yawansu sun rasa rayukansu a yayin tabbatar da hakkin su na yin addini, yin taro na zaman lafiya da kuma 'yancin bayyana ra'ayinsu, wanda baki daya suna cikin sashi na 38, 39 da 40 na tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 (wanda aka yiwa gyara).
"Ayyukan El-Rufai, wadanda ya ke yi da gangan kuma ya ke cigaba da yinsu ba tare da kawo karshensu ba wadanda ke da niyyar kawo karshen 'yan Shi'a, musamman a jihar sa, ta sa dole muka shigar da kararmu a kotun duniya (ICC)."
Ya bayyana cewa dama tuni Harkar Musuluncin ta shigar da kara a dangane da hakan, inda ya bayyana cewa an ma nemi kotun da ta yi bincike tare da yanke hukunci ga shugaban Hafsan sojojin Nijeriya, Janar Tukur Burutai mai ritaya, da duka Kwamishinonin 'yan sanda wadanda suka yi aiki daga shekarar 2015 lokacin da El-Rufai ya fara mulki a matsayin gwamna.
Dakum ya yi ikirarin cewa Burutai da duka Kwamishinonin 'yan sanda wadanda suka yi aiki a karkashin mulkin El-Rufai a tsawon shekara takwas, an yi imanin cewa sun taimaka wajen aikata wadannan laifuffuka.
Saboda haka sai Bala ya yi roko ga gwamnati mai zuwa da kada ta ba El-Rufai kowanne matsayi a gwamnatin tarayya, kamar yadda aka ba Burutai matsayin ambasada a karkashin mulkin Buhari domin kada a shafawa kasar bakin fenti.
Post a Comment