Header Ads

Gwamnatin tarayya ta amince da a yi amfani da rigakafin zazzabin cizon sauro na R21 Matrix

Allurar riga-kafin cutar maleriya

Gwamnatin Nijeriya ta amince da a yi amfani da wani sabon rigakafin zazzabin cizon sauro wanda masana a jami'ar Oxford suka kirkiro mai suna R21 Matrix, inda ta zama ta biyu a duniya bayan kasar Ghana da suka nuna amincewarsu.

Rigakafin, R21/Matrix - M, jami'ar Oxford ce ta kirkiro shi kuma Serum Institute of India ke samar da shi.

Darakta Janar na hukumar kula da abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC), Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja.

Kamar a kasar Ghana, Misis Adeyeye ta bayyana cewa rigakafin na samar da kariya ne daga zazzabin cizon sauro a tsakanin yara 'yan watanni 5 zuwa watanni 36 da haihuwa.

Daraktar ta kara da cewa Nijeriya na sa ran samun rigakafin har guda 100,000 kafin amincewa kasuwa su fara yin shirye-shirye da hukumar kula da lafiya matakin farko a Nijeriya (National Primary Health Care Development Agency).

Rigakafin na R21/Matrix - M, shine rigakafi na biyu wanda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta taba amincewa da shi kuma wanda ya taba bayar da sakamakon da ake so har kashi 75 cikin 100 bayan shafe watanni 12 ana kula da yadda ya ke.

Rigakafin ya samar da sakamakon da ake so har kashi 77 cikin 100 a cikin watanni 12 da aka yi amfani da shi a kan wasu yara a yammacin Afirka, bayan an rinka yi masu allurarsa sau uku.

Rigakafin zazzabin cizon sauro na farko da aka amince da shi, RTS, S ko kuma Mosquirix, daga kamfanin Birtaniya mai yin magunguna na GSK, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta amince ne da shi a cikin shekarar 2021 bayan an kwashe shekaru ana yin aiki a kan sa. Sai dai rashin kudi da rashin kasuwa ya sa kamfanin ya kasa samar da rigakafin kamar yadda ake bukata. 

Bincike daban-daban ya nuna cewa karfin aikin rigakafin na GSK shine akalla kashi 60 cikin 100, kuma yana raguwa a tsawon lokaci ko bayan an yi amfani da wani maganin wanda zai kara masa karfi.

No comments

Powered by Blogger.