Header Ads

Gwamnatin jihar Legas ta zargi sojoji da 'yan sanda da zama manyan masu karya dokokin hanya

Gwamnatin jihar Legas ta gargadi sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a jihar da su gujewa karya dokoki da ka'idojin kan hanya.

Gwamnatin ta bayyana cewa za ta kai rahoton duk wani jami'i daga yanzu wanda aka samu ya na karya dokokin ga hukumar da ta dace.

A cikin wani jawabi wanda Ma'aikatar Sufuri a jihar ta fitar a karshen mako, ta nuna rashin jin dadin ta da yawan karya dokokin hanya wanda sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an da ke sanye da kaki ke yi ba tare da kula ba, inda ta bayyana cewa kowa ya kamata ya bi doka kuma a kowanne lokaci.

Jawabin ya bayyana cewa gwamnatin jihar na cike da mamakin yadda jami'an tsaro wadanda ke sanye da kaki wanda sune ya kamata a ce suna kula da dokokin hanya amma su ke karya su, inda ta bayyana cewa ba za a bari wannan al'amari ya cigaba da faruwa ba tare da kulawa ba.

Sai ta kara da cewa duk wata cutarwa ga jami'an kula da hanya wanda jami'an tsaron za su yi ba za a taba bari ta tafi haka ba.

No comments

Powered by Blogger.