Header Ads

Finland ta zama mambar NATO a hukumance, Rasha ta nuna adawarta

Babban sakataren kungiyar NATO, Jens Stroltenberg (a tsakiya) na yin maraba ga Finland cikin kungiyar NATO bayan Ministan Harkokin Kasashen Waje na Finland, Pekka Haavisto (a hagu) ya mika takardar musamman zuwa ga Sakataren Harkokin Kasashen Wajen Amurka, Antony Blinken.

Kasar Finland ta zama mamba a kungiyar NATO a hukumance duk da gargadi akai-akai daga kasar Rasha, wadda ta dauki alkawarin fuskantar kowacce barazana da yin shirin kara fadada karfin sojan ta a yankin yammaci da arewa-maso-yammacin kasar Nordic din in har hadakar kasashen ta kawo karin sojoji ko wasu kayayyaki cikin sabuwar mambar ta su.

A cibiyar kungiyar ta NATO da ke Brussels, an gudanar da biki a ranar Talata, inda sakataren kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg, Ministan Harkokin Kasashen Wajen kasar Finland, Pekka Haavisto da kuma Sakataren Harkokin Kasashen Wajen Amurka, Antony Blinken, suka kammala duk wasu matakai domin shigar kasar ta Finland hadakar tsaron ta NATO karkashin jagorancin Amurka a gaban manema labaru.

"A yanzu za mu iya bayyana Finland a matsayin mamaba ta 31 a cikin kungiyar Yarjejeniyar Arewacin Tekun Atlanta (NATO)." Blinken ya bayyana bayan Haavisto, wanda shine ya sanya hannu a matsayin kasancewar Finland a cikin kungiyar, ya bayar da takardar Finland ta kasancewa mamba ga takwaransa na Amurka.

A nasa bangaren, shugaban kasar Finland Sauli Niinisto, ya tabbatar da kasancewar kasar cikin kawancen na NATO a cikin wani jawabi da ya gabatar.

"A yau kasar Finland ta zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO. Lokacin kasancewa a ware ya wuce, wani sabon lokaci ya fara yanzu." Ya bayyana.

"Kowacce kasa na kara karfafa tsaron ta, haka ita ma Finland. A matsayinmu na mamba, hakan zai kara mana karfi a cikin kasashen duniya ya kuma samar mana da damar yin shirye-shirye cikin hikima. A nan gaba, Finland za ta samar da na ta taimakon domin samar da kariya da kuma tsaro ga NATO." Kamar yadda shugaban kasar ta Finland ya kara da cewa.

Sai dai a bangaren Rasha, ta mayar da kakkausan martani a ranar Talata, inda ta bayyana cewa kasancewar Finland a kungiyar NATO zai tilastawa Rasha daukar matakai domin fuskantar kowacce barazana.

"Kremlin (fadar gwamnatin Rasha) ta yi imanin cewa wannan zai kara lalata abubuwa ne kawai, kara fadada NATO karin matsaloli ne ga tsaron mu da muradun Rasha. A haka muke kallon al'amarin. Za mu dauki matakai domin fuskantar kowacce barazana domin tabbatar da tsaronmu." Kamar yadda kakakin Kremlin, Dmitry Peskov, ya bayyana yayin wata fira da manema labaru. 

"Ku yarda da ni, sojojinmu za su fada mana duk abinda ke faruwa a kan lokaci...Za mu kula da duk abinda ke faruwa a Finland, yadda kungiyar NATO za ta sa makamai, kayayyaki da na'urori da za su kasance kusa da kan iyakar mu domin yi mana barazana. Sakamakon haka, to a kan hakan za mu dauki matakan." Peskov ya bayyana. 

Kasar Finland ta yi iyaka da kasar Rasha har na tsawon kilomita 1,340 daga bangaren gabashin. Yanzu kuma kan iyakar Rasha da NATO ya kara lunkuwa bayan Finland ta shiga kungiyar tsaron.

No comments

Powered by Blogger.