Fada ya kaure a Sudan a yayin da yawan wadanda suka rasa ransu ya haura mutum 100
Fada a kasar Sudan ya shiga kwana na uku a yayin da 'yan kasar suka farka da karar harbe-harben manyan bindigogi da karar bama-bamai daga jiragen sama, a lokaci daya kuma wadanda suka rasu sakamakon fadan ya kusa kaiwa mutum 100.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, an ji karar fashewar abubuwa a babban birnin kasar ta Sudan, Khartoum, a ranar Litinin, sakamakon fadan da ake yi a tsakanin sojojin kasar da dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF).
"Yawan wadanda suka rasu a tsakanin fararen hula... Ya kai 97." Kamar yadda gamayyar likitoci ta bayyana sannan "wasu" da yawa cikin masu fadan sun rasu wasu kuma sun jikkata.
Kamar yadda rahotannin kafafen watsa labaru suka nuna, wannan adadin bai hada da duka wadanda suka jikkata ba domin da yawa ba za su iya zuwa asibiti ba domin wahalhalu a hanyar tafiya saboda fadan.
Kwamitin likitoci a Sudan, wata kungiya mai goyon bayan damakaradiyya, ta bayyana cewa akwai mutane da dama da suka rasu a tsakanin jami'an tsaro a yayin da wasu 942 suka jikkata.
Fadan wanda ya barke a ranar Asabar a kasar Sudan, an ga yin amfani da hare-haren jiragen sama, tankoki a kan tituna, harbi da manya-manyan bindigogi a wuraren da ke dauke da yawan jama'a a Khartoum da sauran biranen kasar Sudan, hakan kuwa shi ya sa ake ta kiraye-kirayen tsagaita wuta.
Fada dai a Sudan ya barke ne a ranar Asabar a tsakanin sojojin kasar wadanda ke yin biyayya ga Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF) a karkashin mataimakan shugaban Sudan, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hamedt.
Post a Comment