Dubban Mazauna birnin Landan sun bi yi Allah wadai da harin Isra'ila a masallacin al-Aqsa
A tsawon kwanaki biyu, birnin Landan ya shaida wani gagarumin taron jama'a wadanda ke nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a harabar ofishin jakadancin Isra'ila da ke Ingila a yayin da ake cigaba da samun hatsaniya a babban birnin Falasdinawa wanda aka mamaye na Al Quds.
Dubunnan mazauna Landan din sun bi sahun takwarorinsu ne wajen nuna fusatarsu a ranar Juma'a da Asabar bayan wani bidiyo wanda ya nuna sojojin Isra'ila na kai farmaki ga musulmai masu gabatar da ibada a harabar masallaci mai tsarki na al-Aqsa ya watsu a kafafen sada zumunta.
An nuno musulmai Falasdinawa ana dukansu, ana harbinsu, ana wurga masu barkonun tsohuwa (tear gas) a yayin da aka keta alfarmar masallacin mai tsarki.
Dama dai cutarwar Isra'ila a kan musulmai Falasdinawa a cikin wata mai tsarki na Ramadan ba wani abu bane sabo. Ya na faruwa kusan kowacce shekara.
Saidai a wannan karon, masu gudanar da zanga-zanga sun fusata ne sakamakon rashin yin Allah wadai da al'amarin daga kafofin watsa labaru na yammacin duniya.
"A lokacin da al'amarin kasar Ukraine ya faru, kowa na maganar, akwai tutocin Ingila a kowanne wuri, duka suna magana a kai, sun sa kayan tutocin Ukraine, amma da ya zo kan Falasdinawa, wanda ke faruwa shekaru da dama, ni zan ce kawai wariyar launin fata ne.
"A yayin kwallon kafa? Sun sa tutocin Ukraine a kowanne wuri, kambun da ke kafadar kaftin ma an sa Ukraine a wurin.
"Amma da abin ya zo kan Falasdinawa sai suka ce kada a sa siyasa a cikin kwallon kafa, akwai nuna son kai sosai." Kamar yadda ya ke a cikin wani jawabi da Batool al-Subeiti, wata mai fafutika, ta yi.
Mamaye kasar Falasdinawa ta fara ne tun cikin shekarar 1948 a yayin da kasashen turai suka fara mamaye kasar da niyyar kirkirar kasar Yahudawa.
Yakin da ake yi a Ukraine bai wuce shekara daya ba, amma yadda kafofin watsa labarun yamma suka dauki al'amurran ya banbanta matuka.
Rasha ta fuskanci takunkumin tattalin arzuki da al'adu da sadarwa, a yayin da Isra'ila ke cigaba da samun kyakkyawar dangantaka da kasashen turai da kuma Amurka.
To saidai hare-haren Isra'ilan ba su tafi hakanan ba, domin kuwa makaman roka da aka harbo daga Gaza da kuma kudancin Lebanon sun haifar da razana a cikin Isra'ila.
Zaman dar-dar na cigaba a yayin da ake tunanin Isra'ila na iya cigaba da musgunawar da ta ke yi.
Post a Comment