Header Ads

Cutar sankarau: Ana zaton mutane 212 sun kamu, a yayin da wasu 23 suka mutu a jihohi uku

Ana kyautata zaton mutane 212 sun kamu da cutar sankarau a yayin da wasu mutane 23 suka mutu a jihohi uku da ke Nijeriya.

Cutar sankarau dai cuta ce wadda ke kumbura fatocin da ke lullube da kwakwalwa da kuma kashin baya (spinal cord).

A cikin wani sabon rahoto da ta fitar a ranar Asabar, hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta bayyana cewa yawan wadanda ake kyautata zaton sun kamu a cikin sati na 13, daga 27 ga watan Maci zuwa 2 ga watan Afirilun shekarar 2023, ya karu da kashi 8 cikin 100 in an kwatanta da satin da ya gabata na 12 (196).

Rahoton na hukumar ta NCDC ya nuna cewa jihar Jigawa ke da kashi 62 cikin dari 100 na wadanda ake kyautata zaton sun kamu da cutar a yayin da jihohin Yobe da Adamawa ke da kashi 17 cikin 100 kowannensu. 

Hukumar ta ma bayyana cewa mutane 23 sun rasu sakamakon cutar inda jihar Yobe ke da mutane 17 jihar Jigawa kuma 9.

Hukumar ta bayyana cewa sashe na musamman na hukumar zai cigaba da bibiyar yadda abubuwa suke kasancewa a cikin jihohi.

Baki daya, daga sati na 40 na shekarar 2022 zuwa sati na 13 na shekarar 2023, wadanda ake kyautata zaton sun kamu da cutar sune mutane 1,479 a yayin da mutane 118 suka rasu, wanda ke nuni da kashi 9.3 cikin 100 da aka yi rahoto daga jihohi 22 a lokacin da ake fama da cutar.

"An dauki samfuri na mutane 512, an kuma tabbatar da cewa mutane 235 na da cutar, inda kashi 46 a cikin 100 aka tabbatar da cutar ce tun farkon shigowar lokacin cutar a cikin shekarun 2022/2023." Kamar yadda hukumar ta NCDC ta bayyana.

Hukumar hana yaduwar cututtukan ta bayyana cewa 'yan shekaru 5 zuwa 14 ne suka fi kamuwa da cutar, a yayin da maza suke da kashi 57 cikin 100, mata kuma kashi 43 cikin 100. 

A kan yadda cutar ke iya yaduwa kuwa, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa kwayar halittar "bacteria" da ke yada cutar sankarau na iya yaduwa a tsakanin mutum-zuwa-mutum ta hanyar digon ruwan da ke cikin hanyoyin numfashi ko miyau na wadanda suka kamu.

Yin kusa da majina ko tarin wanda ya kamu ko zama a harabar da wanda ya kamu ya ke na tsawon lokaci ko kayayyakin da ya ke amfani da su za su iya yada cutar kamar yadda hukumar ta nuna, inda ta kara da cewa tsakatsakin kyankyasar cutar shine kwanaki hudu, amma za ta iya kyankyashewa a cikin kwanaki biyu zuwa goma.

No comments

Powered by Blogger.